Binciken Gaskiya: EFCC Ba Ta Kama Dan Peter Obi Bisa Laifin Zamba Ba
- Wani mai amfani da shafin Facebook, Shamsuddeen Lawal Hussain ya yada wani labarin da ke cewa, da ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour ya shiga hannun EFCC bisa laifin zama
- Hussain ya yi tsokaci ne kan wani rubutun EFCC da ke cewa an kama wani Tope Peter Obi bisa aikata zamba
- Binciken da muka yi ya nuna gaskiyar wanene Tope Peter Obi, kuma mun gano ba da bane ga dan takarar shugaban kasa Peter Obi ba
Najeriya - Shamsuddeen Lawal Hussain, wani mai amfani da shafin Facebook ya yi zargin an kama wani matashi da aka ce da ne ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi.
A rubutun da muka gano, Shamsuddeen ya ce, hukumar EFCC ta kama matashin ne mai suna Tope Peter Obi, wanda a ikrarinsa wai da ne ga dan takarar shugaban kasan jam'iyyar Labour.
Ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
"Dan Peter Obi ya shiga komar EFCC."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tushen ikrarin Shamsuddeen
Shamsuddeen dai na tsokaci ne ga wani kamun da hukumar EFCC ta yi na ba da labarin yadda aka daure wani matashi dan damfara bisa laifin aikata zamba.
A rubutun na EFCC, an ce mai shari'a O.A Okunuga na babban kotun jihar Legas ya daure matashin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba, inda zai shafe shekara guda a magarkama.
An gurfanar da matashin ne bisa laifi daya; mallakar takardun da ya yi amfani dasu wajen aikata zamba.
A cewar mai shari'a, laifin matashin ya saba da sashe 318 na kundin manyan laifuka ta jihar Legas, 2011.
Matashin ya amsa laifinsa, daga nan aka daure shi shekara daya ko kuma ya biya N500,000.
Shin Tope Peter Obi da ne ga dan takarar shugaban kasan jam'iyyar Labour, Peter Obi?
Yayin da bincike ya nuna kamanceceniya a sunayensu, amma babu wata hujja da ke nuna Tope da ne ga dan takarar shugaban kasa Peter Obi
Legit.ng ta yi duba ga cikakkiyar sanarwar da EFCC ta fitar a shafinta na yanar gizo da na sada zumunta. Babu inda hukumar ta ce Tope dan Peter Obi na jam'iyyar Labour ne.
Daily Trust ta tabbatar da binciken cewa, Tope Peter Obi ba dan Peter Obi na jam'iyyar Labour bane.
A cewar jaridar, Peter Obi na da 'ya'ya biyu ne kadan; Gabriella Nwamaka Francis Obi da Gregory Peter Oseloka Obi.
Kakkabe batu: Ba a kama dan Peter Obi da laifin rashawa ba
Binciken da ke sama zai tabbatar da cewa, wanda aka kama ba dan Peter Obi na jam'iyyar Labour bane, kawai sunaye ne suka yi kama da juna.
Ghanim Al-Muftah: Abubuwa 8 Masu Jan Hankali Game da Matashin Da Ya Jika Zukatan Jama'a a Bude Wasan WC a Qatar
Dan Peter namiji dai sunansa Gregory Peter Oseloka Obi, ba Tope Peter Obi ba kamar yadda aka yada.
EFCC ta sha gurfanar da 'yan siyasa da 'ya'yansu a Najeriya, a makon da ya gabata aka sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yero bisa zargin Rashawa.
Asali: Legit.ng