Rabuwar Kan Shugabannin Kiristocin Arewa: Jerin Wadanda Suka Watsawa Babachir Kasa A Ido

Rabuwar Kan Shugabannin Kiristocin Arewa: Jerin Wadanda Suka Watsawa Babachir Kasa A Ido

A ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya sanar da cewa Kiristocin Arewa sun yi ittifakin goyon bayan dan takaran shugaban kasan jam'iyyar Labour Party, Peter Obi.

Kungiyar Kiristocin sun yi tarayya ne kan nuna rashin amincewarsu da tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Babachir David Lawal shine shugabansu kuma mafi akasari yan jam'iyyar APC ne.

Dogara
Rabuwar Kan Shugabannin Kiristocin Arewa: Jerin Wadanda Suka Watsawa Babachir Kasa A Ido Hoto: Yakubu Dogara, Peter Obi
Asali: Facebook

Bayan matakai daban-daban da suka dauka na ganin cewa Tinubu ya zabi daya daga cikin yan siyasar Arewa kuma Kirista a matsayin mataimakinsa ya ki cimma gaci, Lawal ya sanar da cewa yanzu suna bayan Peter Obi.

Amma wasu mambobin kungiyar suka ce ba dasu Lawal yayi wannan shawara ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

An samu rabuwan kai tsakanin Kiristocin Arewa: An Watsawa Babachir Lawal kasa a ido

Jim kadan bayan sanarwar, wasu jiga-jigan kungiyar takwas suka fitar da sakon nesanta kansu da Babachir Lawal..

A wasikar kar-ta-kwana da suka fitar da daren Alhamis, 24 ga Nuwamba, mambobin kungiyar kimanin goma karkashin jagorancin tsohon Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara sun yi hannun riga da Babachir.

Sun bayyana cewa marawa Peter Obi baya ra'ayinsa ne kawai kuma ba na kungiyarsu ba.

Ga jerin wadanda suka kwancewa shugabansu zani a kasuwa:

  1. Tsohon Kakain majalisa, Yakubu Dogara,
  2. Tsohon mataimakin gwamnan Kogi, Simon Acbuba
  3. Hon. Albert Atiwurcha
  4. Prof Doknan Sheni
  5. Mela A. Nunge, SAN,
  6. Gen Ishaya Bauka (rtd)
  7. Prof Ibrahim Haruna
  8. Mrs Leah Olusiyi.

Tikitin Musulmi da Musulmi: Tinubu Da Shettima Ba Za Su Dandana Mulkin Najeriya Ba a 2023, inji Babachir Lawal

A wani labarin mai alaka da wannan, SGF Babachir Lawal, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) da dan takarar, Asiwaju Tinubu Bola ba za su kai labari ba a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Kara Karfi a Arewa, Jiga-Jigai da Wasu Yan Takarar Majalisa Sun Koma APC

Lawal ya ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba zai yi nasara a zabe mai zuwa ba saboda zaban Kashim Shettima musulmi dan uwansa da yayi a matsayin abokin takara.

Babachir ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da sashen Hausa na BBC.

Ya tuhumi Tinubu da watsi da Kiristocin Arewa kuma yana ganin ko babu su zai isa lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida