Shugaban Jam’iyyar APC Yana Tsoron Amfani da Na’urorin Zamani a Zaben 2023
- Shugaban jam’iyyar APC yana ganin akwai matsala wajen amfani da na’urar zamani a harkar zabe
- Abdullahi Adamu ya bayyana damuwarsa a lokacin da suka zanta da kungiyar kasashen renon Afrika
- Sanata Adamu yana ganin ana fama da karancin wuta da abubuwan more rayuwa da za su iya kawo cikas
Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu yana da ta-cewa a game da amfani da fasahohin zamani wajen shirya zaben 2023.
Sanata Abdullahi Adamu ya nuna shakkunsa ne a lokacin da ya zauna da tawagar kungiyar da ke kula da kasashen da ke karkashin rainon Birtaniya.
Tribune ta rahoto cewa Abiola Sunmonu ta jagoranci ‘yan tawagarta da za su sa ido a zaben Najeriya zuwa sakatariyar jam’iyyar APC da ke garin Abuja.
Adamu yana ganin cewa zai yi wahala wadannan nau’rori su iya aiki da kyau a lokacin da ‘Yan Najeriya suke ta fama da karancin wutan lantarki.
An kawo na'urorin zamani
Tribune Online tace INEC za tayi amfani da BVA da IReV domin a tantace masu kada kuri’a kafin suyi zabe da kuma daura sakamakon zabe a yanar gizo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jama’a za su iya amfani da shafin IReV domin ganin sakamakon zaben 2023 kai-tsaye. Sabuwar dokar zabe ta amince ayi amfani da na’urorin nan.
Korafin Shugaban APC
"Na farko, na taba zama Sanata, abin da ya dame mu shi ne tanadin da muka yi na amfani da wadannan fasahohi ta bangaren aika sakamako kai-tsaye.
Aika sakamako a kowane bangaren Najeriya yana bukatar karfin hawa yanar gizo. Na san har a yankunan birnin Abuja akwai inda babu karfin sabis.
Sannan kuma a bangarori da-dama na kasar nan, akwai karancin wutar lantarki. Dole hukumar INEC ta bamu tabbaci 100 bisa dari cewa sun shirya.
Dalili kuwa sun yi maganar yi wa batiransu caji, amma a baya an yi zabukan da suka ce an gaza caji.
- Abdullahi Adamu
Daily Trust ta rahoto Sakataren gudanarwan APC na kasa, Ambasada Suleiman Argungu, yana cewa na’urorin zamanin ba za su iya aiki a kauyensu ba.
An karbe mana jirgi - Obi
An samu labari cewa ana shirin baro filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, sai hukuma ta bada umarnin karbe jirgin saman Obidient.
An yi niyyar amfani da jirgin saman zuwa wajen taron yakin zabe a garin Ibadan, a karshe sai dai aka nemi wani jirgin saman dabam da aka je yawon kamfe.
Asali: Legit.ng