Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Matashin Da Ya Bude Wasan Cin Kofin Duniya da Karatun Al-Qur’ani
- Wan matashi, Ghanim Al Muftah ya sace zukatan mutane da dama bayan ya saki gagarumin sako a yayin bude taron wasan FIFA 2022
- A yayin bikin, matashin ya hau munbari a filin wasa na Al Bayt tare da jarumin Hollywood Morgan Freeman
- Sakin daddadan sako da karatun Qur'ani da matashin yayi a taron ya burge masoya da masu kallo
Qatar - Duk da tawayar halitta da yake da shi, wani matashi ya ja hankalin duniya bayan ya isar da gagarumin sako da karatun al-Qur'ani a wajen bude taron cin kofin Duniya na FIFA.
Matashin mai suna Ghanim Al Muftah ya burge masoya da masu kallo yayin da ya hau kan munbari tare da shahararren jarumin Hollywood Morgan Freeman a filin wasa na Al Bayt a kasar Qatar.
Kasancewar ya zama sha kallo ga matasa da dama, ba a san abubuwa da dama ba game da Ghanim Al Muftah.
A wannan zauren, Legit.ng ta gabatar da wasu abubuwa takwas da ya kamata a sani game da shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
1. An haife shi a Mayun 2002
An haifi Ghanim Al-Muftah a ranar 5 ga watan Mayun 2022, yanzu shekarunsa 20.
2. An haife shi da nakasa
An haifi matashin da nakasa ta musamman wanda ke hana barin jikinsa daga kasa girma.
3. Ya yi kuruciyarsa cikin hali na rashin tabbass ga rayuwa
Bayan haihuwarsa, likitoci sun nuna cewa da kyar zai dade a raye. An fadama iyayensa cewa ba zai rayu fiye da shekaru 15 ba, amma sai gashi ya fi hakan. Ga shi har ya kai shekarar 2022.
4. Ya kasance dan kasuwa mafi kankantar shekaru a Qatar a 2017
Kasancewarsa mai shafin Youtube, mai wayar da kan jama'ar kuma shugaban wani cibiyar siyar da asikirin, Ghanim Al Muftah ya zama dan kasuwa mafi kankantar shekaru a Qatar a 2017. Ya kuma kasance mai aikin taimako.
5. Yana samun kulawar likitoci duk shekara a lasar Turai
Sakamakon halin da yake ciki, Ghanim Al Muftah yana tafiya kasar Turai duk shekara don samun kwararrun likitoci suyi masa aiki.
6. Yana da miliyoyin mabiya a Soshiyal midiya
Ghanim Al Muftah na da miliyoyjn masu binsa a shafinsa na soshiyal midiya. A shafinsa na Instagram, @g_almuftah, yana da mabiya fiye da miliyan 3.2.
Yana da mutum fiye da 800k da ke bibiyar shafinsa na Youtube.
7. Yana daya daga cikin jakadun FIFA na 2022
An nada Ghanim Al Muftah a matsayin jakada a gasar cin kofin duniya na 20222 da ke gudana a yanzu haka, lamarin da ya kai shi ga shiga harkokin bude taron da aka kammala kwanan nan.
Bayani: Abin Da Ya Kamata Kowane Ɗan Najeriya Ya Sani Game Da Harrufan Larabci A Sabbin Takardun Naira
8. Yanzu haka yana karatunsa na digiri
Tare da burinsa na son zama dan diflomasiyya kuma firai minstan Qatar a nan gaba, matashin na karatun kimiyar siyasa yanzu haka a jami'a.
Asali: Legit.ng