Murkushe Boko Haram Ne Mafi Girman Alherin da Buhari Zai Bari, in Ji Gwamnatin Tarayya
- Ministan harkokin cikin gida ya bayyana cewa, tuni gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen magance faruwar harin magarkama a Najeriya
- Gwamnatin Najeriya na alfahrin sanar da cewa, babban abin da shugaba Buhari zai bari shine tarihin murkushe 'yan Boko Haram
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan magarkamar Kuje a babban birnin tarayya Abuja
Abuja - Babban abin alherin da shugaba Buhari ya yiwa Najeriya shine tumbuke jijiyar Boko Haram daga tushe, kamar yadda ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana a jiya Talata.
Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumomi sun kammala bincike kan harin da 'yan ta'adda suka kai magarkamar Kuje da ke Abuja a watannin baya kadan da asuka gabata.
Aregbesola ya bayyana hakan ne a wani taron baje-kolin nasarorin gwamnatin Buhari da aka gudanar a Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.
Gwamnatin Tarayya Ta Gama Bincike, Ta Gano Mutanen da Suka Kitsa da Ɗaukar Nauyin Fashin Gidan Yarin Kuje
Ya shaida cewa, a yanzu dai babu wata karamar hukuma da take hannun tsagerun Boko Haram, lamarin da kai tsaye ke nuna nasarar murkushe tsagerun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
"A 2015, mambobin Boko Haram ke da ikon wasu kananan hukumomi a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, amma yau an fatattake su.
"A yau an murkushe tada zaune tsaye a kasar mu. Wannan zai iya zama babban abin da za mu bari. Wannan zai zama babban abin da shugaba Buhari zai bari."
An kammala bincike kan harin magarkamar Kuje
A bangare guda, ministan ya yi tsokaci game da nasarar da hukumomi suka yi na bincike kan abin da ya faru a magarkamar Kuje a watannin baya.
Ya kuma bayyana cewa, tuni an ba shugaba Buhari cikakken rahoton, kuma zai duba don daukar mataki na gaba.
Hakazalika, ya ce an sake kamo da yawan wadanda suka gudu yayin da 'yan ta'adda suka kai harin, Leadership ta ruwaito.
Ya kuma yi alkawarin cewa, ba za a sake samun irin wannan tashin hankali ba a Najeriya a nan gaba.
An farmaki magarkamar Kuje
A baya kunji yadda 'yan ta'addan Boko Haram suka farmaki magarkamar Kuje tare da sakin wasu mambobinsu da dama, sun saki bidiyon yadda suka kai harin.
'Yan Najeriya sun shiga tashin hankali tun bayan wannan hari, lamarin da ya ya kai kasashen waje na daukar matakan kiyaye kai a Abuja.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda lamarin ya faru tare da bayyana irin matakan da ake dauka don gujewa faruwar harin a gaba.
Asali: Legit.ng