Mutum Ya Ba da Labari Mai Ban Mamaki Na Yadda Ya Mutu Kuma Ya Dawo Duniya
- Wani dan Najeriya ya ba da labarin yadda Allah ya warkar dashi daga wani rashin lafiya da ya yi mai kisa
- A wani bidiyon da aka yada a TikTok, mutumin mai suna Solo Akinsanya ya ce, ya kwanta rashin lafiya ne bayan halartar bikin abokinsa
- Solo ya kwanta a asibiti, inda aka yi masa gwaje-gwaje masu yawa tare da gano yana dauke da cutar dajin hanji, kuma jikinsa na kara tsanani
Najeriya - Wani dan Najeriya mai suna Solo Akinsanya ya ba da labarin yadda ya bakunci kiyama amma ya dawo da nufin Allah.
A wani bidiyo mai daukar hankali da aka yada a TikTok, mutumin ya bayyana dalla-dalla yadda ya kwanta rashin lafiya aka garzaya dashi asibiti.
Ya ce, ya shiga yanayi na tsananin ciwo da ke nuna akwai mummunan abu mai girma da ke faruwa dashi.
Lamarin jikinsa ya yi muni, har wasu asibitoci suka ki karbarsa yayin da ya zama abin Allah sarki. A cewarsa, kawai dai ya ma mutu ne saboda jinin jikinsa ya kare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga karshe, ya ce an yi masa gwajin hanci a asbitin koyarwa na jami'ar jihar Legas, nan aka tabbatar da yana da dajin hanji.
Amma duk da haka, yace Allah ya ba shi lafiya, da aka sake gwada shi, aka tarar ciwon dajin da ake zato ya riga ya kau. Likitoci sun firgita da wannan lamari.
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a
@georginaibeh yace:
"Abin da Allah ba zai iya yi ba, to tabbas babu shi."
@eveify yace:
"Jinjina ga Almasihu!!!!! Tabbas abin da ALlah ba zai iya ba babu shi."
@misslisa___007 yace:
"Abin da ka gani zai tabbata da yardar Yesu."
@lauryella yace:
"Abin ALLAH ba zai iya ba tabbas babu shi. Alkawarin Allah ya tabbata a kanta. Godiya ta tabbata ga Allah."
@1fabulous_gall tace:
"Idan dai akwai dan adam din da zai addu'a. Akwai Allahn da zai amsa. Abin da Allah ba zai iya ba dai babu shi."
Yaro ya mutu ya dawo a cocin Fasto Suleman
A wani labarin kuma, wani bidiyo ya nuna lokacin da wani mutum ya gabato da dansa ga shahararren faston Najeriya, Suleman tare da bayyana cewa ya mutu ya dawo.
Wannan lamari dai ya faru ne a wani bikin addinin Kirista da aka gudanar a birnin Benin, kamar yadda rahotanni suka shaida.
Jama'a sun shiga jazama yayin da aka shiga godiya ga ubangiji kan wannan al'amari mai mamaki da ya faru.
Asali: Legit.ng