Wasu Fasinjoji Da Suka Taso Daga Gombe Zuwa Legas Sun Kone Kurmus

Wasu Fasinjoji Da Suka Taso Daga Gombe Zuwa Legas Sun Kone Kurmus

  • Wasu rahotanni da muka samu da safiyar Talatan nan sun nuna cewa an samu wani mummunan hatsari a Titin Abuja-Lokija
  • Akalla Fasinjoji 17 suka ƙone kurmus wasu hudu suka jikkata bayan sun taso daga Gombe da nufin zuwa Legas
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra na Abuja ya alaƙanta abinda ya jawo hatsarin da gudun wuce ƙa'ida

Abuja - Fasinjoji 17 dake hanyar zuwa jihar Legas Sun kone ƙurmus a wani hatsarin Mota da ya auku a babban Titin Abuja-Lokoja da Safiyar Talatan nan.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa mutane huɗu daga cikin Fasinjojin waɗanda suka taso daga jihar Gombe, Allah ya sa da sauran numfashinsu a gaba sun tsira da saurukan wuta.

Rahotanni sun nuna cewa Jami'an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) sun ɗauki mutanen da hatsarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Abaji domin kula da su.

Kara karanta wannan

'Yan Daba Sun Kai Farmaki Wurin Gangamin Yakin Neman Zaben Atiku a Gombe, Sun Yi Ɓarna

Hatsarin Mota ya yi ajalin mutane.
Wasu Fasinjoji Da Suka Taso Daga Gombe Zuwa Legas Sun Kone Kurmus
Asali: Original

Wani shaida, Kabir Garba, yace hatsarin ya rutsa da wata Motar Bas Toyota Hiace mai ɗaukar mutum 18 da lambar Rijista GME 20 XA da kuma Babbar Tirela Daf mai lamba BAU 632 XA

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Motocin sun yi karo da juna a kusa da Yaba junction da ke kan babban Titin Abuja zuwa Lokoja.

Yace Motar Bas ɗin wacce ta fito daga Titin Abuja-Gwagwalada da gudun tsiya, ta bugi Tirelar ta baya kana ta tarwatse filla-filla.

Wakilin jaridar wanda ya dira wurin da misalin karfe 7:23 na safe ya gano cewa Jami'an kwana-kwana na fafutukar kashe wutar yayin da dakarun FRSC ke kokarin zaro gawarwakin da suka ƙone.

Legit.ng Hausa ta fahimce cewa jami'an FRSC sun maida hanyar matafiya zuwa hannu ɗaya ga motocin da zasu nufi ɓangaren gabashin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Hadimin Gwamnan APC

Menene ya haddasa Hatsarin?

Da aka tuntuɓe shi, kwamandan FRSC na birnin tarayya Abuja, Mr Samuel Ogar Ochi, ya tabbatar da faruwar mummunan hatsarin.

A ruwayar Channels tv, Kwamandan ya alaƙanta abinda ya haddasa Hatsarin da gudun wuce ƙima da Direban Motar Bas ɗin ya yi da kuma rashin ganin gabansa.

Yace hukumarsa zata haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da jami'an duba gari domin duba yadda za'a yi wa mamatan Jana'iza da binne su sakamakon sun ƙone ta yadda ba za'a iya tantance su ba.

Mista Ochi ya gargaɗi masu Motoci musamman waɗanda ke tafiyar dare su guji gudun da ya zarce ƙa'ida duba da yanayin lokacin Buji da ake ciki, wanda a cewarsa ke haddasa rashin gani sosai.

A wani labarin kuma Ayarin Motocin Kwamishinan Jihar Bauchi Sun Yi Hatsari Mai Muni, An Rasa Rayuka

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa Hatsarin ya rutsa da Motar dake cikin Ayarin kwamishinan da wata ta haya, mutum biyu suka ce ga garinku nan.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wani Mutumi Ya Lakaɗa Wa Matarsa Duka Har Lahira Kan Karamin Saɓani

Ancewa kwamishinan kananan hukumomin Bauchi da taimakanon yan sanda da jami'an FRSC ne suka yi aikin ɗaukar waɗanda abun ya shafa zuwa Asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262