Ayarin Motocin Kwamishinan Jihar Bauchi Sun Yi Hatsari Mai Muni, An Rasa Rayuka

Ayarin Motocin Kwamishinan Jihar Bauchi Sun Yi Hatsari Mai Muni, An Rasa Rayuka

  • Jerin gwanon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi sun yi hatsari a kan hanyarsu ta zuwa taron siyasa
  • Bayanai sun nuna cewa mutum biyu sun rasa rayuwarsu sakamakon haɗarin wanda ya auku a kan titin Miya-Wurji, karamar hukumar Ganjuwa
  • Kwamishinan, Abdulrazaq Nuhu Zaki, da jami'an FRSC ne suka ɗauki waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibiti

Bauchi - Wani mummunan hatsari ya rutsa da Ayarin kwamishinan kananan hukumoni da harkokin naɗin sarauta na jihar Bauchi, Abdulrazaq Nuhu Zaki,

Jaridar Tribune Online tace Hatsarin wanda ya rutsa da motocin cikin Ayarin da dama ya lakume rayukan mutum biyu a kan hanyarsu ta zuwa Warji halartar taron siyasa.

Taswirar jihar Bauchi.
Ayarin Motocin Kwamishinan Jihar Bauchi Sun Yi Hatsari Mai Muni, An Rasa Rayuka Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Haka nan wani mutum ɗaya ya jikkata, ya samu karaya a ƙafarsa ɗaya da kuma kananan raunuka a ilahirin jikinsa yayin hatsarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 2:25 na rana.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sifetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Gana da Jiga-Jigan Siyasa 18 a Abuja

A wani rahoto da hukumar kiyaye haɗurra reshen jihar Bauchi ta fitar ta hannun Ofishinsu na Ganjuwa, ta tabbatar da faruwar hatsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton, Hatsarin ya faru da karfe 2:25 na rana kuma hukumar ta karɓi rahoto da ƙarfe 2:30 sannan jami'an FRSC sun isa wurin da ƙarfe 2:35, wanda a cewar rahoton Minti 5 kacal jami'ai suka ɗauka.

Wani sashin rahoton yace:

"Hatsarin ya auku a Titin Miya-Wurji a garin Miya, ƙaramar hukumar Ganjuwa, mutum biyar lamarin ya rutsa da su, ɗaya ya ji raunuka biyu kuma sun rasa rayuwarsu."
"Motoci biyu ne hatsarin ya rutsa da ɗaya ta ma'aikatar kananan hukumomin jihar ce, ɗayar kuma ta haya ce kuma wani Muhammad Mu'awiya ne ke tuƙata. Asalin abinda ya jawo shine saɓa wa dokar gudu."

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni aka kawar da waɗanda lamarin ya shafa zuwa babban Asibitin Kafin Madaki domin kula da lafiyarsu da tabbatar da waɗanda suka mutu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali, Bayan Yayi Tatil da Giya, Kofur Ya Buge Babban Janar Da Mota Har Lahira

Jaridar Punch tace Hukumar FRSC tare da taimakon shi kansa kwamishinan kananan hukumomi, AbdulRazak Nuhu da yan sanda ne suka ɗauke mutanen daga wurin zuwa Asibiti.

An Kama Wata Mota Makare da Bindigogi Zasu Shiga Harabar Babbar Kotun Jihar Osun

A wani labarin Dakarun tsaro dake binciken masu shige da fice a babbar Kotun Osun sun kama wata mota makare da Bindigu da mutane

Wani ganau ya bayyana cewa nan take yan sanda suka tasa motar da waɗanda ke ciki zuwa sashin binciken manyan laifuka na hedkwatar yan sanda Osogbo.

Sai dai mai magana da yawun hukumar yan sandan Osun ta fitar da sanarwar cewa babu wani abun tada hankali domin an gano mutanen dake cikin motar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel