ASUU ta Fito da Sabon Salo a Sakamakon Haramtawa Malaman Jami’a Yajin-Aiki
- Kungiyar malaman jami’o’i za ta sa kafar wando daya da gwamnatin tarayya a kan batun albashi
- ASUU tace dole ne a biya su albashin watanni 8 da aka yi a lokacin da aka yi yajin-aiki a jami’o’i
- Gwamnatin Najeriya tace ba za ta biya kudin ayyukan da ba ayi ba, amma ‘Yan ASUU suna da ja
Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i watau ASUU, suna barazanar tsallake zangon karatun da aka samu a tangarda a dalilin dogon yajin-aikin da aka yi.
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa idan har gwamnatin tarayya ta ki biyan malaman jami’a albashinsu, za su tsallake zangon karatun da ya shude.
Wasu malaman jami’ar UNIPORT ta jihar Ribas sun bayyana cewa ba za ta yiwu a hana su kudinsu ba tun da dai suna biyan bashin karatun da ya wuce.
Malaman sun ce a halin yanzu sun gwamutsa karatuttukan zango mai-ci da wanda ya shude.
Ana rigima a kan albashin watanni 8
Gwamnatin tarayya tace ba za ta biya ‘yan ASUU kudin aikin da ba suyi ba, amma malaman jami’o’in gwamnati sun ce ba za su yarda da wannan tsari ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar ‘ya ‘yan kungiyar na ASUU, ana biyan malamin jami’a albashinsa ne duk wata, ba jinga ake yi da shi na daidai gwagwardon ayyukan da ya yi ba.
"Domin mun san duk Duniya babu inda ake biyan malaman jami’a kamar ma’aikatan wucin-gadi.
Saboda haka muka gayyaci iyaye, da kuma dalibai domin mu sanar da su yadda abubuwa suke tafiya tun da muka janye yajin-aikinmu.
Tun da muka dakatar da yajin-aiki a sakamakon umarnin kotun kwadago, mun koma bakin aiki. muna biyan bashin abida ya taru mana.
Muna rama ayyukan da ya kamata a ce mun yi a lokacin yajin aiki. A matsayin masu ilmi, ba mu yarda da tsarin ‘babu aiki-babu albashi ba.”
Ba karantarwa kadai muke yi ba
“Saboda a lokacin da ake yajin-aiki, muna yin bincike. Karantarwar ne kurum ba muyi. Mun yi bincike da aikin taimakawa al’umma.
Karantarwar da ba mu yi ba, ga shi nan muna yi a yanzu. Muna biyan bashin ayyukan da ke kanmu."
- Wani malamin jami'a
Zanga-zanga a Jami'o'i
A makon da ya gabata aka samu labari ‘Yan Kungiyar ASUU za su shiga zanga-zanga da nufin nunawa gwamnatin tarayya rashin jin dadinsu kan hana su albashi.
ASUU tace za tayi zanga-zanga, kuma a tsaida karatu saboda zaftare masu albashi da aka yi a Oktoba. Hakan ya biyo bayan rashin nasarar da suka samu a kotu.
Asali: Legit.ng