Osinbajo Zai Ziyarci Kasar da Babu Shugaban Najeriya da Ya Je a Fiye da Shekaru 20

Osinbajo Zai Ziyarci Kasar da Babu Shugaban Najeriya da Ya Je a Fiye da Shekaru 20

  • An yi shekaru sama da 20 ba a ji labarin wani Shugaban Najeriya ya ziyarci kasar Kanada ba
  • A makon nan Yemi Osinbajo ya tafi kasar, zai yi muhimman taron da za su taimaki Najeriya
  • Farfesa Osinbajo zai gana da Mataimakiyar Firayim Minista, Taurari da kuma ‘Yan kasuwa

Abuja - A karshen makon jiya aka ji Farfesa Yemi Osinbajo zai bar Abuja zuwa kasar Kanada, inda ake sa ran zai shafe wasu ‘yan kwanaki a can.

Jaridar The Cable tace Mataimakin shugaban kasar zai zama shugaban farko da ya ziyarci kasar Arewacin Amurkan tun bayan Olusegun Obasanjo.

Ana sa ran wannan ziyara za ta karfafa alakar Najeriya da Kanada, domin Yemi Osinbajo zai samu damar haduwa mataimakiyar Firayin Minista.

Baya ga Chrystia Freeland, Osinbajo zai yi zama na musamman da manyan ‘yan majalisa da sauran jami’an gwamnatin Kanada yau a garin Ottawa.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai

Najeriya za ta amfana

A tsawon kwanaki uku da zai yi, mataimakin shugaban Najeriyan zai tattauna da takwarorinsa a kan harkokin ilmi, fasaha, hadin-kai da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Farfesan zai gabatar da jawabi a jami’ar Queen’s University da ke Kingston a ranar Laraba a game da yadda ake neman cin ma manufofin UN SDGs.

Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo a hanyar Kanada Hoto: @akandeoj
Asali: Twitter

Rahoton yace Osinbajo zai zauna da jami’ar Carleton, makasudin wannan zama shi ne yadda za a inganta bincike da kuma manhajar karatu a Najeriya.

Har ila yau, shugaban zai sadu da kungiyoyin ‘Yan Najeriya da ke zama a Kasar wajen da jami’an gwamnatin Kanada da suka fito daga kasar nan.

Premium Times idan an kammala wannan, Farfesa Osinbajo zai dawo garin Abuja a cikin makon nan. Laolu Akande ya tabbatar da wannan a Twitter.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

‘Yan kasuwa da masu zuba hannun jari a kasar Amurkan suna cikin wadanda za a zauna da su.

Citizens Network For Peace and Development in Nigeria

An ji labari Francis Okereke Wainwei yace tun da Goodluck Jonathan bai samu takara a zaben 2023 ba, Kungiyar CNPDN suna tare da Bola Tinubu.

Wannan kungiya da suka sayawa Goodkuck Jonathan fam din neman takarar shugaban kasa ba su yarda mulki ya cigaba da zama a Arewa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng