Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matashin Malami a Jihar Kwara, Sun Nemi Fansa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matashin Malami a Jihar Kwara, Sun Nemi Fansa

  • Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, Sun yi awon gaba da matashin Malami da ɗansa a jihar Kwara
  • Bayanai daga mahaifin waɗanda aka sace, Imam Amolegbe, yace maharan sun nemi kuɗin fansa daga wurinsu
  • Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar yace suna kan bincike kuma sun kama mutum 2 da ake zargi

Kwara - Miyagun 'yan bindiga sun kai samame yankin Oko-Olowo, wata unguwa dake gefen Ilorin, babban birnin jihar Kwara da safiyar ranar Asabar, sun sace mutane uku.

Mutanen da harin ya shafa sun haɗa da wani matashin Malami, Alfa Sofiu Amolegbe, ɗan uwansa da ake kira, Fasansi da kuma ɗansa Aliyu.

Leadership ta tattaro cewa masu garkuwan sun farmaki mutanen ne a gidansu da ke Oko-Olowo, kan babban Titin Ilorin-Jebba kuma sun kutsa gidan ne ta taga.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wasu Gwamnoni Sun Kama Hanyar Ficewa Daga PDP? Atiku Ya Yi Magana

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matashin Malami a Jihar Kwara, Sun Nemi Fansa Hoto: leadership
Asali: Twitter

Ɗan uwan Malamin, Fasansi ya yi yunkurin guduwa amma 'yan bindigan suka harbe shi tare da daba masa adda sannan suka barshi jikin jini.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mahaifin waɗanda aka sace, Imam Amolegbe of Dada, Limamin yankin Okelele, yace maharan sun bar Fasansi a zatonsu ya sheƙa barzahu amma a yanzu yana kwance a wani Asbitin kuɗi a Ilorin.

Shin sun nemi kuɗin fansa?

Imam Amolegbe ya bayyana cewa 'yan bindigan sun tuntubi iyalai kuma sun nemi a haɗa musu miliyan N100m a matsayin kuɗin fansa.

Yace:

"Masu garkuwan sun tuntuɓemu kuma sun nemi Miliyan N100m, mun rokesu su karɓi miliyan N10m duk da bamu da su."
"Ina rokon gwamnatin Kwara da mutane masu fatan Alheri su taimaka mana mu kubutar da 'ya'yana biyu da jikana daga hannun waɗannan miyagun."

Legit.ng Hausa ta gano cewa tun bayan jin labarin mutane suka fara tururuwar zuwa jajantawa Uban waɗanda aka sace, wanda ya kasance babban Malami a Anguwar.

Kara karanta wannan

Kano: Sabbin Bayanai Masu Taba Zuciya Sun Fito A Zaman Shari'ar Ɗan China da Ya Kashe Ummita

Wasu makusantan Shehin Malamin sun fara Addu'a domin Allah ya kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun 'yan sandan Kwara, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da kai harin, yace tuni suka kama mutum 2 da ake zargi da hannu a garkuwa da 'ya'yan malamin.

"Muna cigaba da bincike kan lamarin kuma muna gab da kubutar da su . A halin yanzun mun kama mutum 2 da ake zargi," inji shi.

A wani labarin kuma tsagerun Yan Bindiga Sun Sheke Jami’an Yan Sanda Uku a jihar Enugu

Rahotanni sun bayyana cewa wasu miyagun sun halaka dakarun 'yan sanda har uku a kan bakin aikinsu a jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya.

Lamarin wanda ya auku a shingen binciken yan sanda dake Agbani ya tada hankulan mutane sakamakon yadda maharan suka buɗe wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262