'Yan Sandan Kebbi Sun Ceto Mutum 7 Daga Hannun ’Yan Bindiga, Sun Kama Tsageru 3 da Ake Zargi

'Yan Sandan Kebbi Sun Ceto Mutum 7 Daga Hannun ’Yan Bindiga, Sun Kama Tsageru 3 da Ake Zargi

  • 'Yan sanda a jihar Kebbi sun yi nasarar ceto wasu mutanen da 'yan bindiga suka sace suka tafi dasu bayan bata-kashi da suka yi a wasu yankunan jihar
  • An kama wasu mutum biyu da ake zargi fa ta'ammuli da kudaden jabu, tuni rundunar 'yan sandan suka fara bincike
  • Yankunan Arewacin Najeriya na fama da rikicin 'yan bindiga, lamarin da ya daidaita jama'a da dama da gidaje da dukiyoyinsu

Jihar Kebbi - 'Yan sandan jihar Kebbi sun yi nasarar ceto mutum bakwai daga hannun gungun 'yan ta'adda biyu a yankunan Bena-Mairairari da Ruwan Kanwa a kananan hukumomin Danko Wasagu da Jega a jihar.

Wannan na fitowa ne daga bakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora a Birnin-kebbi yayin gabatar da 'yan ta'addan ga manema labarai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: 'Yan sanda sun kamo kasurguman 'yan bindiga 16 da suka addabi Zamfara

Ya bayyana cewa, jama'arsa sun yi bata-kashi da 'yan bindigan a Bena-Mairairai kafin daga bisani suka ceto mutum uku; Jamila Ahamad, Shamsiyya Ahamad da Tasi'u Haruna.

Ya kuma bayyana cewa, an gano wata moto kirar Toyota Corolla mai lambar DTF 236 LP mallakin 'yan bindigan da kuma wasu kayayyaki.

An ceto wadanda aka sace a Kebbi
'Yan Sandan Kebbi Sun Ceto Mutum 7 Daga Hannun ’Yan Bindiga, Sun Kama Tsageru 3 da Ake Zargi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani bangaren kuma na ci gaba da ragargazar tsagerun, kwamishinan ya bayyana cewa, jami'an tsaro sun ceto wasu mutum hudu da ke hannun 'yan bindiga a yankin Jega na jihar.

An kama wani mutum da kudin bogi

A wani yankin, an kama wani Bashiru Sani na yankin Helende a karamar hukumar Argungu dauke da wasu kudade na jabu.

A cewar kwamishinan:

"'Yan sanda sun kama wanda ake zargin kudade 'yan N1,000 na jabu da suka kai N316,000.
"A yayin bincike, babban wanda ake zargi, wani Samaila Umar, wanda ya buga kudaden shi ma ya shigo hannu."

Kara karanta wannan

Luguden NAF Ya Halaka Manyan Yan Bindiga 3 da Ake Nema da Mayankansu a Jihohin Arewa

Mazauna a Arewa maso Yammacin Najeriya sun yi imanin cewa, maboyar 'yan bidinga ba biyayye bane, ya kamata a tabbatar da kama su tare da hallaka su, kamar yadda suka shaidawa Daily Trust.

An kama kasurgumin dan bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma kunji cewa, a makon da ya gabata ne aka gabatar da wani babban dan bindiga a jihar Zamfara tare da wasu mutum 16 da ake zargin su ma 'yan bindiga ne.

An kuma gurfanar da wasu mutanen da ake kyautata zaton 'yan fashida dai sauran ayyukan laifuka da suka saba doka.

Ana ci gaba da kakkabe 'yan ta'adda a yankuna daban-daban na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.