Jami’a ta Yaye Tsohon Ministan Buhari, Ya Kammala Digiri Bayan Komawa Gaban Malamai
- Rotimi Chibuike Amaechi ya kammala karatun digirin farko daga jami’ar Baze da ke babban birnin Abuja
- Tsohon Ministan sufurin na tarayya ya samu shaidar LLB watau Digiri a ilmin shari’a a makon nan
- ‘Dan siyasar yana cikin dalibai 504 da aka yaye da suka yi karatu a bangarorin ilmi dabam-dabam
Abuja - Tsohon Ministan tarayya, Rotimi Chibukwe Amaechi yana cikin daliban da aka yaye daga jami’ar nan ta Baze da ke garin Abuja.
Rotimi Chibuike Amaechi wanda ya rike kujerar Ministan sufuri na kusan tsawon shekaru bakwai ya tabbatar da hakan a shafin Twitter.
Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan siyasar ya wallafa hotunansa dauke da alkyabbar kammala jami’a a ranar Asabar, 19 ga Nuwamba 2022.
Amaechi yana cikin dalibai 504 da aka yaye daga wannan jami’ar kudi bayan sun yi shekaru hudu zuwa shida suna karatun digirin farko.
Biyo bayan kawo karshen karatun na su, The Cable tace an ba wadannan dalibai takardar shaidar samun ilmin digirin farko daga jami’ar.
An yi yaye na 9 a Baze
Wannan ne karo na tara da jami’ar ta yaye dalibai tun bayan kafa ta a shekarar 2011.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakan yana nufin tsohon gwamnan ya samu ilmin da ake bukata da tarbiyya a tsawon zamansu a jami’ar duk da karancin lokacinsa.
Anya kuwa?
Amma malaman jami’a irinsu Farfesa Abdulgaffar Abdulmalik Amoka suna ganin akwai ta-cewa a tattare da digirin tsohon Ministan.
Da yake magana a shafinsa na Facebook cikin gatse, Farfesan ya yi mamakin yadda Amaechi ya yi karatu alhali yana kan kujerar Minista.
Deji Adeyanju ya samu LLB
Kamar yadda Vanguard ta fitar da rahoto, shahararren ‘dan gwagwarmayar nan, Deji Adeyanju yana cikin abokan karatun Rotimi Amaechi.
Shi Kwamred Deji Adeyanju ya fito da matakin farko (watau First Class) daga jami’ar, yayin da Hon. Amaechi ya samu mataki mai bi masa (2’1).
Amaechi bai taba zuwa Jami'a ba?
Kafin yanzu, a shekarar 1987 Rotimi Amaechi ya samu shaidar Digirin B.A a bangaren ilmin Ingilshi da kuma Adabi daga jami’ar Fatakwal.
A lokacin yana dalibin jami’ar UNIPORT. Amaechi ya rike kujerar shugaban kungiyar daliban jihar Ribas, daga baya ya shiga siyasa da kyau.
Mutuwar Priscilla Sitienei
An samu labarin Priscilla Sitienei wanda tana neman shekara 100 da haihuwa, ta shiga makarantar boko a kasar Kenya ta rasu a makon jiya.
Ana saura kwanaki uku wannan tsohuwa ta rasu sai da ta je aji. Marigayiya Sitienei ta rasu a lokacin da ake shirin fara jarrabawar firamare.
Asali: Legit.ng