Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Tonon Arzikin Man Fetur Na Farko A Arewa
- Jihohin Arewa biyu zasu shiga jerin jihohin Najeriya masu arzikin man fetur mai dinbin albarka
- An yi kiyasin cewa arzikin danyen man da aka gano a Bauchi da Gombe ya kai ganga bilyan daya
- An fara neman azikin man a jihar Borno amma matsalar rashin cewa ya tilasta dakatar da aikin
Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata zai jagoranci kaddamar da hakan arzikin man fetur na farko a tarihin Arewacin Najeriya.
Za'a fara hakan arzikin mai a jihar Bauchi da Gombe.
Wannan hakar arzikin mai da zai kasance a Kolmani (OPL) 809 da 810.
Shekaru biyu da suka gabata aka gani arzikin man fetur a Arewa.
Gabanin gano arzikin, yankin Neja Delta kadai ke da arzikin man fetur a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun 2016, NNPC ta fara neman arzikin mai a wasu jihohin Najeriya kuma aka samu nasara a Bauchi, Gombe, Borno da Neja.
A cewar hukumomi a NNPC, kamfaonin da aka baiwa kwangilan hakan mai sun hada da Sterling Global Oil, New Nigeria Development Commission (NNDC) and NNPC Limited.
Daily Trust ta ruwaito wani jami'in gwamnati da cewa:
"Bikin fara tonon zai gudana ne ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba kuma shugaban kasa da kansa zai halarta tare da yawancin ministocinsa fari da karamin Ministan man fetur, Timipre Sylva."
Rahotanni sun nuna cewa arzikin man dake yankin Kolami ya kai gangan bilyan daya kuma wannan zai taimakawa Najeriya matuka wajen samun kudi.
Wannan sabon arziki na zuwa ne lokacin da Najeriya ke fama da karancin danyen mai sakamakon barayin mai da suka addabi bututu a Neja Delta.
Zan Cire Tallafin Man Fetur Idan Nayi Nasara a zabe: Tinubu
A wani labarin, Asiwaju BolaAhmed Tinubu, mai takarar kujerar shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar, All Progressives Congress (APC), ya ce zai cire tallafin man fetur idan yayi nasara ya hau mulki.
Tinubu ya bayyana hakan ne takardar manufofinsa da ta yadu.
Dan siyasa ya ce cikin wata shida na farko zai aiwatar da sabuwar dokar PIA, zai cire tallafi kuma zai samar da wasu sabbin ka'idoji don janyo hankalin masu zuba jari.
A cewarsa;
"Zamu cire tallafin man fetur amma zamu samar da hanyoyin taimakawa mutane."
Asali: Legit.ng