‘Yan Sanda Sun Sheke ‘Yan Bindiga 7 a Wata Arangama a Neja
- Jami’an ‘yan sanda tare da hadin guiwar ‘yan sa kai da mafarauta sun ragargaji ‘yan bindiga a Neja inda suka halaka bakwai daga ciki
- Mazauna yankin Kumbashi dake karamar hukumar Mariga ta jihar sun hanzarta kiran jami’an tsaro bayan ganin ‘yan bindiga na musu karakaina
- Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin yace wasu daga cikin ‘yan bindigan sun arce da miyagun raunika yayin da wasu ‘yan sa kai aka kai su asibiti bayan sun jigata
Niger - Mazauna Kumbashi dake karamar hukumar Mariga ta jihar Neja a ranar Alhamis sun fuskanci karuwar farmakin ‘yan bindiga yayin da ‘yan sandan jihar suka yi mummunan artabu da ‘yan bindiga a yankin.
Majiyoyi daga kauyen sun sanarwa Channels TV cewa ‘yan sandan sun kwashe gawawwakin ‘yan ta’adda masu tarin yawa bayan arangamar.
A yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun yace arangamar da aka yi ta hada da ‘yan sanda tare da ‘yan sa kai da ‘yan bindigan kuma an halaka ‘yan bindigan 7.
Abiodun yayi bayanin cewa, bayan ganin ‘yan bindigan, mazauna yankin sun hanzarta sanar da jami’an dake yankin wanda hakan ya janyo mutuwar ‘yan bindigan bakwai duka da wasu sun tsere da raunika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sahara Reporters ta rahoto cewa, sai dai yace ‘yan sa kai biyu da suka samu raunika an mika su babban asibitin Kontagora domin samun kulawar likitoci.
Yace:
“Sakamakon gamsassun bayanan sirri da muka samu kan cewa ‘yan bindigan dake addabar manoma wuraren Kumbashi an gansu suna zarya a garin Kumbashi, jami’an tsaron sun yi ruwan wuta kansu tare da fin karfinsu.
“Har ila yau, a cigaba da kakkabe ta’addanci, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifi a Neja, rundunar ‘yan sanda tare da mafarauta da ‘yan sa kai dake zama a Kumbashi sun yi arangama da ‘yan bindiga kuma sun halaka bakwai yayin da sauran sun tsere daji da raunika.”
’Yan bindiga sun kai asibitin Neja
A wani labari na daban, ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai farmaki cikin babban asibiti a jihar Neja.
Basu daga kafa ba bayan sun gama harbe-harbe sun tasa keyar wasu ma’aikatan lafiya tare da yin garkuwa da wasu mutane.
Asali: Legit.ng