‘Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Plateau, Sun Halaka Mutum 11

‘Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Plateau, Sun Halaka Mutum 11

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kai kazamin farmaki yankin Maikatako dake karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau inda suka halaka mutum 11
  • An gano cewa miyagun sun kai kazamin farmakin wurin karfe 1 na daren Laraba inda suka dinga harbi da kone gidajen mazaunin yankin
  • Wani mazaunin yankin yace har yanzu ba a tabbatar da yawan wadanda suka halaka ba sannan ‘yan bindigan sun koma wurin karfe 8 na safe

Plateau - A kalla mazauna 11 wasu miyagun ‘yan bindiga suka halaka a yankin Maikatako dake shiyyar Butura dake karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Taswirar Plateau
‘Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Plateau, Sun Halaka Mutum 11. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa, maharan sun zo wurin karfe 1 na daren Laraba kuma sun fara harbi babu kakkautawa tare da kone gidaje.

Jama’a da yawa an gano sun samu miyagun raunika a harin baya ga wadanda aka halaka da gidajen da aka kurmushe.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Fada, Sun Halaka Wani Sarki da Fadawansa a Najeriya

Wani mazaunin yankin mai suna Daniel Isah, yace mazauna yankin har yanzu suna kokarin tantance adadin wadanda aka halaka inda ya kara da cewa an babbaka wasu ta yadda ba a gane su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A halin yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutum 11.”

- Ya kara da cewa.

Daily Trust ta rahoto cewa, yace maharan sun dawo yankin wurin karfe 8 na safe inda suka cigaba da harbe-harbe. Yace har yanzu jami’an tsaro basu kawo musu dauki ba.

Rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa, 9 daga cikin mamatan duk ‘yan gida daya ne.

An tuntubi ‘yan sanda

Kiraye-kirayen da ake ta yi wa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, Alabo Alfred, ya nuna cewa yana kan waya kuma bai yi martani kan sakon kar ta kwana da aka aika masa ba a yayin rubuta wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Kaduna: Luguden Wutan Jiragen NAF Yayi Ajalin ‘Yan Bindiga, Wasu Mutane Sun Kubuta

’Yan bindiga na cin karensu babu babbaka

Miyagun ‘yan bindiga suna cin karensu babu babbaka har yanzu a wasu sassan kasar nan.

A cikin kwanakin karshen makon nan ne miyagun suka shiga har fadar wani basarake inda suka halaka shi da fadawansa, lamarin da ya tura jama’ar yankin da duk wadanda labarin ya riska.

Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah wada da faruwar lamarin mai bada takaici inda yayi umarni da a tsamo wadanda suka yi mugun aikin.

Ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta tsamo su kuma su ladabtar dasu da hukuncin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel