Gwamnatin Tarayya ta Gyara Rangyem din ‘Yan Makaranta, Ta Kara N30 kan Kowanne Kwanon Dalibi
- Gwamnatin tarayya tayi gyara kan tsarin ciyar da dalibai inda aka mayar daga N70 na kowanne dalibi zuwa N100 na abincinsu
- Kwamishinan jin kai da walwala na jihar Delta yace gwamnatin tarayyan tayi hakan ne domin sake inganta nagartar abincin da daliban ke ci
- Ya rarrabewa masu girki kayan aiki wanda yace su yi amfani da nagartattun halayensu don su zame musu jagora wurin aikin da aka saka su
An sake duba shirin ciyar da yaran makaranta a Najeriya inda aka duba shi tare da kara N30 kan N70 na kudin abincin ‘yan makaranta a jihar Delta.
Punch ta rahoto cewa, kwamishinan jin kai da tallafi, Dakta Darlington Ijeh, wanda ya bayyana hakan a Asaba, ya bayyana takaicinsa kan yadda masu dafa abincin ke kauro.
Ijeh, wanda aka Gwamna Ifeanyi Okowa ya rantsar a watan Augustan 2022, ya sha alwashin lura da shirin gwamnatin tarayyan domin inganta rayuwar jama’ar jihar.
Kwamishina ya bayyana kalubalen da ya fuskanta game da ciyarwar ‘yan makaranta
Yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Bayan shigata ofis a watanni uku da suka gabata, na gaji wasu lamurran koma baya daga NHGSFP da ya hada da rashin biya kan lokaci, da sauran matsalolin da suka shafi masu girkin wadanda ke taba dalibai da jiha.
“A yau an sake duba N70 na abincin kowanne ‘dan makaranta inda aka mayar N100 kowanne da kuma sauran matsalolin da suka addabi tsarin ciyar da ‘yan makaranta a jihar kamar rashin masu girkin da biya ba bisa tsari ba, sun zama tarihi.”
Kwamishinan wanda ya raba kayan abinci ga masu girkin yayi kira garesu da su mayar da halayya tagari ta zama jagoran aikinsu, Within Nigeria ta rahoto.
Yace tsarin ciyarwan an yi shi ne domin ciyar da ‘yan makarantun gwamnati daga aji 1 zuwa 3 inda ya kara da cewa an yi hakan ne domin karfafa guiwar iyaye wurin sanya yara a makaranta tare da inganta abincin dalibai.
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari
FG ta saba ciyar da ‘yan makaranta
Gwamnatin tarayya ta dade tana ciyar da ‘yan makaranta abincin rana amma daga ‘yan aji daya zuwa aji uku.
Wannan ya kasance wani lamari dake karawa yaran kwarin guiwa wurin zuwa makarantar.
Asali: Legit.ng