An Tasa Keyar Fasto Gidan Yari Bisa Zargin Damfarar Malamin Makaranta N3m
- Kotu ta tasa keywar wani fasto zuwa magarkama bisa zargin ya ci kudin wata malamar makaranta a jihar Legas
- An kamo faston ne bayan da ya gudu, inda dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana dalla-dalla abin da ya faru
- Fasto ya musanta zargin da ake masa, daga nan aka tasa keyarsa zuwa magarkama har sai ya cika ka'idar beli
Jihar Legas - Wani Raymond Akala Ayodele mai shekaru 36 ya shiga hannun hukuma an kuma gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin ya karbi N3m na wata malamar makaranta mai zaune a Ikorodu a jihar Legas, Mrs Omowumi Arowosegbe.
Ayodele ya yi kirarin cewa, shine babban manajan ERIIFEi Divine Global Enterprise kuma fasto ne shi. Jami'an sashe na 2 na rundunar 'yan sandan jihar Legas sun damke shi, PM News ta ruwaito.
A cewar 'yan sanda, Ayodele, wanda kuma ya yi ikrarin shi tsohon ma'aikacin Friesland Capena ne da ke Ogba a Legas, ana zargin ya karbi kudade daga matar da sunan zai yi kasuwanci da kudin kana su raba riba.
An ruwaito cewa, bayan da matar ta tura masa kudi a asusun banki, kawai aka nemi Ayodele aka rasa, inda ya cika wandonsa da iska tare da kudin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Fasto ya fece da kudin da yace zai yi kasuwa dasu
Bayan jin shuru, matar ta kai batun ga 'yan sanda ta hannun mataimakin sufeto janar na sashe na 2 a Legas, shi kuwa ya tura jami'ai su kwamuso malam fasto.
Tuni 'yan sanda suka yi himma, suka tabbatar da kamo Ayodele daga maboyarsa tare da damka shi ga magarkama.
An gurfanar dashi a gaban kotun Majistere ta Tinubu da ke tsibirin Legas bisa laifuka guda biyu da suka hada da karbar kudi ta hanyar sharara karya da kuma sata.
Dan sanda mai gabatar da kara SP Ibrahim Haruna ya shaidawa kotu cewa, mutumin ya aikata laifukan ne a cikin watan Fabrairun 2022, Within Nigeria.
Haruna ya shaidawa kotu cewa, Ayodele ya karbi kudade N3m daga malamar da sunan zai suba su a kasuwanci su raba riba, amma ya yi fecewarsa.
An ba da belin fasto bisa sharadi
Haruna ya kuma shadawa kotu cewa, laifukan da Ayodele ya aikata abin hukuntawa a karkashin kudin laifuka da hukunci na jihar Legas, sashe na 314(1) da 287, 2015.
Sai dai, wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, mai shari'a Mrs Ggajumi Ayoku ta ba da belinsa a kan kudi N750,000 tare da kawo masu tsaya masa mutum biyu.
Ayoku ta kuma daga ci gaba da zaman sauraran karar zuwa ranar 7 ga watan Disamba, tare umartar a tsare Ayodele har sai ya cika ka'idar beli.
A wani labarin kuma, an kama ma'aikatan gwamnati, ciki har da wadanda suka yi ritaya bisa zargin sace kudin gwamnati.
Asali: Legit.ng