Soja Ya 'Haukace' A Borno, Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Ma'aikaciyar Bada Agaji, Ya Raunata Direban Jirgi
- Wani sojan Najeriya da ke yaki da yan ta'addan Boko Haram ya bude wuta ya kashe abokin aikinsa a Borno
- Har wa yau sojan ya kuma halaka wata ma'aikaciyar jinya sannan ya raunata mataimakin matukin jirgi na UN
- Daga bisani dai abokan aikinsa sojoji sun bindige shi har lahira don kada a bar shi ya cigaba da barna, an kuma fara bincike
Jihar Borno - Dakarun sojoji na 25 Task Force Brigade sun bindige wani soja wanda ya bude wuta, ya kashe abokin aikinsa da ma'aikaciyar agaji daya kamar yadda Zagazola ya rahoto.
An tattaro cewa sojan wanda ke aiki ta runduna ta musamman ya baro sansaninsa da ke garin Damboa a Borno, misalin karfe 3 na ranar Alhamis kuma ya fara bude wuta da bindigarsa AK-47.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani majiya daga UN ya shaidawa Zagazola Makama, masanin nazarin yaki da ta'addanci da tsaro a Tafkin Chadi cewa faruwar lamarin ya saka fasinjoji da ke jira su shiga jirgi mai saukan ungulu don komawa Maiduguri sun ja da baya sun nemi wurin buya don tsira da ransu.
Majiyoyi sun ce bayan ya karar da harsashinsa, sojan ya fito da wuka ya caka wa ma'aikaciyar Medecins du Monde da ke aiki a Najeriya, ya halaka ta kafin ya raunta matukin jirgin saman.
Daga nan sojan ya juya ya doshi takwarorinsa kafin aka bindige shi don kiyaye cigaba da afkuwar bala'i.
Majiyoyi sunce matukin jirgin da fasinjojinsa sun dawo Maiduguri lafiya yayin da matukin ke asibiti yana samun sauki.
Martanin Rundunar Operation Hadin Kai
A martaninta, Rundunar Operation Hadin Kai ta yi nadamar sanar da al'umma abin bakin cikin da ya faru a saninsanin mu a yau, The Punch ta rahoto.
Manjo Samson Nantip Zhakom, mataimakin direkta na sashin watsa labarai na sojoji, hekwatan Operation Hadai kai ya magantu kan lamarin ya ce wani soja ya kashe ma'aikacin NGO da ke bada agaji a Arewa maso gabas.
Zakom ya ce:
"Wannan sojan ya kashe wani soja daban kuma ya raunata mai taimakawa matukin jirgi na UN. Dakarun mu nan take suna bindige sojan da ya kauce hanya.
"Mataimakin matukin jirgin da ya samu rauni ya samu sauki yayin da gawarwakin an kai su asibitin 7 division.
"An fara gudanar da sahihin bincike tare da daukan matakan kawo gyara kan abin bakin cikin."
Jarumin ‘Dan Banga Ya Harbe ‘Yan Bindiga da Suka Bude Wuta a Kasuwa a Zamfara
A ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba 2022, ‘dan sa-kai na kato-da-gora yayi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Daily Trust ta rahoto cewa wani ‘dan kato-da-gora ya nemi ya hana ‘yan bindiga kai hari a kasuwar Gidan Goga a karamar hukumar Muradun.
Asali: Legit.ng