Anyi Gwanjon Tsofaffin Takalman Biloniya kan N96.6m Bayan Sama da Shekaru 50 da ya Saka su

Anyi Gwanjon Tsofaffin Takalman Biloniya kan N96.6m Bayan Sama da Shekaru 50 da ya Saka su

  • Takalman da Steve Jobs ya saka a tun lokacin da aka fara kirkiro Apple an siyar dasu a kan $218,750 wacce tayi daidai da N96.6 miliyan a gwanjonsu da aka yi
  • Kamar yadda aka yi gwanjonsu a ranar 14 ga watan Nuwamba, Jobs ne ya saka Birkenstocks a shekarun 1970 zuwa 1980 a cikin tarihin Apple
  • Takalman da suka zo daga kamfanin Marks Sheff an siyar dasu a matsayin takalma mafi tsada a tarihin gwanjon takalma da aka taba yi a duniya

Birkenstock suna daya daga cikin kaya mafi kwalisa da ake dasu a Vogue kuma masoyan takalman fata basu tunanin asara idan sun zuba makuden kudade sun siya asalin Birkenstocks.

Takalman Steve Jobs
Anyi Gwanjon Tsofaffin Takalman Biloniya kan N96.6m Bayan Sama da Shekaru 50 da ya Saka su. Hoto daga Steve Jobs, Julien Auction
Asali: UGC

Alamu na nuna babu kudin da za a biya a ce takalman sun yi tsada ballantana idan zufar da ta nitse a cikin takalman ta Steve Jobs ce, mamallakin kamfanin Apple.

Kara karanta wannan

Kamfanin da Tinubu Yace Ya yi wa Aiki a kasar Waje Sun Ce Ba Su San Shi ba

Takalman Birkenstock din masu launin ruwan kasa an siyar dasu kan N96.6 miliyan wanda yayi daidai da $218,750 a wani gwanjo da aka yi a birnin New York a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda gwanjon Juliens ya bayyana, tsohon ‘dan kasuwan ya saka takalman a shekarun 1970 zuwa 1980 yayin da ake ta kokarin ganin kafuwar kamfanin Apple.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Birkenstocks sun zo daga kamfanin Mark Sheff, wanda ke kula da rukunin gidajen Albany Calif na Job a shekarun 1980.

Darakta Martin Nolan yace an fara siyar da takalman kan kudi da ya kai N883,000 a shekarar 2016.

Kamar yadda NPR ta bayyana, gwanjon ya hada da hotunan NFT na Birkenstocks a matsayin kayayyakin siyan.

An siyar da wasikar neman aiki ta Steve Job a sama da N83m

Kara karanta wannan

Yadda Wani Mai Kudin Bitcoin Ya Zama Talaka Dare Daya

Steve Job, marigayi tsohon mamallakin kamfanin Apple ya shiga kanun labarai amma a wannan lokacin kan abinda yayi ne sama da shekaru 50 da suka gabata.

Rubutacciyar wasikar neman aikin da ya rubuta a shekarar 1973 an siyar da ita kan $222,400 wacce tayi daidai da N83,983,420 daga kamfanin gwanjo na Charterfields.

Kamfanin gwanjon na Chatterfield sun tabbatar da cewa Jobs da hannunsa ya rubuta wasikar neman aikin. Sai dai wasikar bata bayyana wacce jiha yake son yin aiki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel