Hotunan Yadda Gobara Ta Laƙume Dukiyoyin 'Miliyoyi' A Kasuwar Singer Ta Kano
- Gobara ta lakume kayayyakin masarufi a wani dakin ajiyar kaya a kasuwar Singer da ke Kano
- Kasuwar ta yi fice ne wurin sayar da kayayyakin masarufi kamar madara, biskit, alawa, fulawa da sauransu kan sari
- Wani ma'aikacin kamfanin da ke dajin ajiyarsu ya kone ya ce ba tabbatar da sanadin gobarar ba amma ana zargin lantarki ne
Jihar Kano - An yi gobara a kasuwar Singer da ke birnin Kano a safiyar ranar Talata 15 ga watan Nuwamban shekarar 2022.
Wani shago inda ake ajiye biskit da alewa ba zato ba tsammani ya kama wuta a kasuwa, wacce ke daya daga cikin mafi yawan jama'a a jihar.
A halin yanzu jami'an kashe govara a jihar suna kokarin kashe wutar, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasuwar Singer galibi ana siyar da kayan sari ne da suka kada da fulawa, taliya, lemun kwalba da sauransu.
Daily Trust ta rahoto cewa dakin ajiyar kayan da ya kama da wuta na Mimza General Enterprises ne.
Wani ma'aikacin kamfanin da gobarar ta yi barna ya magantu
Muhummad Abdullahi, wani ma'aikaci a kamfanin ya ce ba a san sanadin gobarar ba amma ana zargin matsalar wutar lantarki ne.
Ya ce:
"Shine babban dakin ajiyar kayayyaki na kamfanin, galibi ana ajiye cin gam, alawa, madara da wasu abubuwa. Ba zamu iya cewa ga abin da ya haddasa gobarar ba. An kira ni da safen nan cewa shagon mu ya kama da wuta, hakan yasa na yi gaggawar zuwa don in ga abin abin da ke faruwa.
"Ba zan iya kiyasta abin da aka rasa ba, amma dai miliyoyin naira ne don ko jiya an sauke kayan miliyoyi."
Ga wasu hotunan gobarar a kasa:
Hotunan Yadda Gobara Ta Yi Mummunan Ɓarna A Sashin NOUN A Jigawa
A wani rahoton, gobara ta cinye sashin Jami'ar karatu daga gida ta Najeriya, NOUN, da ke Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar.
Rahotanni sun ce gobarar wacce ta faru a ranar Asabar 12 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ta kona kayayyakin ofis da wasu abubuwa a sashin.
Hukumar kwana-kwana na jihar da ta tarayya da Dutse International Fire Service ne suka taru suka kashe gobarar, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng