An Kama Dan Takarar Gwamna da Ke Shirin Tserewa Abuja, an Tura Shi Gidan Yarin Fatakwal
- Tsohon dan takarar gwamna ya shiga hannun hukuma bisa zargin ya sace kayayyakin da suka kai miliyan 800
- An gurfanar dashi a gaban kotu, inda mai shari'a ya umarci a mika shi magarkama ba tare da bata lokaci ba
- Ana yawan samun 'yan siyasa da zargin sata ko rashawa a Najeriya, lamarin da ya zama ruwan dare a kasar
Jihar Anambra - Tsohon dan takarar gwamnan jihar Anambra, Walter Okeke wanda ke kan umarnin kamu daga kotun majisteren Fatakwal bisa zargin sata ya shiga hannun jami'an tsaro, tuni an tura shi magarkama.
Mai shari'a AO Amadi-Nna ya ba da umarnin kama shi ne a ranar Litinin a Fatakwal tare da cewa Okeke ya mika kansa kafin karfe 11:25 na safe, Daily Sun ta ruwaito.
Dan sanda mai gabatar da kara, Godday Amadi ya shaidawa kotun yadda jami'an 'yan sanda suka samu nasarar kamo Okeke tare da yadda aka kawo shi gaban kotu.
Ba tare da bata lokaci ba, mai shari'a ya tasa keyar Walter Ubaka Okeke zuwa magarkamar Fatakwal har zuwa ranar 8 ga watan Disamba don sake sauraran shari'ar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da ake zargin Okeke da aikatawa
Ana zargin cewa, Okeke ya saci kayan kudi daga kayayyakin hakar mai da sauran kayayyaki masu muhimmanci da kudinsu ya kai N800m.
A tun farko, shari'ar ta zo da gargara yayin da Okeke ya garzaya babbar kotu don tabbatar da hakkinsa na dan adam, amma hakan ya gaza, daga nan kuma bai halarci zaman kotun majisteren ba.
Okeke, wanda dan asalin kauyen Enugwu ne a karamar karamar hukumar Orumba ta Anambra, yana rayuwa ne a gidansa da ke yankin Trans Amadi a Fatakwal, kuma an ce a can ya boye kayayyakin da ake zargin ya sata.
Lamarin dai ya faro ne tun lokacin da wanda ya shigar da kara, Ifeanyi Amaonye ya bayyana cewa, ya nemi kayayyakinsa ya rasa, kuma yana zargin Okeke na da hannu a ciki, This Day ta ruwaito.
'Yan sanda sun shiga lamarin, daga nan aka zarce kotu, inda ta ba da umarnin kamo Okeke tare da gurfanar dashi a gabanta.
Kotu ta umarci a kamo dan takarar sanatan jihar Kano
A wani labarin kuma, wata kotu ta umarci a kamo dan takarar sanatan Kano ta tsakiya, Abdulkareem Abdulsalam Zaura bisa zargin damfarar wani dan kasar waje.
Kafin umarnin kotun, an kai ruwa rana da AA Zaura, wanda mamban jam'iyyar APC ne kkan zargin da ake masa.
Kotun ta ce a kamo shi ne saboda ya ki halartar zaman kotu a shari'ar da ake ci gaba da yi dashi a Kano.
Asali: Legit.ng