Sojoji 2 da Wasu Mutum 5 Sun Halaka Yayin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Garin Gwamna

Sojoji 2 da Wasu Mutum 5 Sun Halaka Yayin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Garin Gwamna

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kai kazamin hari kan sojojin Najeriya a Isuofia dake karamar Hukumar Aguata a jihar Anambra
  • A take suka halaka sojoji biyu yayin da aka yi hanzarin aike jami’an tsaro wurin, sojin sun halaka ‘yan bindiga biyar a take yanke
  • Isoufia wanda shi ne kauyensu Gwamna Chukwuma Soludo, yana cigaba da fuskantar kazamin hari daga ‘yan bindiga wanda hakan yasa aka girke jami’an tsaro

Anambra - A kalla mutum bakwai ake tsammanin sun sheka lahira a yankin Isoufia, asalin garinsu Gwamna Chukwuma Soludo, yayin da aka yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da sojoji.

Anambra Gunmen
Sojoji 2 da Wasu Mutum 5 Sun Halaka Yayin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Garin Gwamna. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wadanda aka gano sun rasa rayukansu a karamar hukumar Aguata ta jihar Ribas din sojoji biyu ne da ‘yan bindiga hudu.

Kamar yadda aka sanar da jaridar The Nation, lamarin ya faru ne a safiyar Asabar a garinsu Gwamna Soludo mai suna Isuofia.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda Sun Dakile Farmakin da ‘Yan Fashi da Makami Suka kai kan Motar Banki a Anambra

The Nation ta tattaro cewa sojoji biyu ‘yan bindigan suka fara halakawa kafin jami’an tsaron su hanzarta zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

’Yan Sanda sun magantu kan farmakin

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi.

Yace:

“An shawo kan lamarin kuma an halaka ‘yan ta’adda biyar yayin da sojoji da ‘yan sandan dake sintiri suka tsananta tsaro a yankin.
“Tawagar hadin guiwar ta samo ababen hawan da suke amfani dasu wurin kai hari da suka hada da Venza da sauransu.
“Za a yi karin bayani kan yadda lamarin yake saboda har yanzu aikin ake yi.”

- Yace.

Sai dai wani babban jami’in ‘dan sanda a jihar wanda ya bukaci a boye sunansa yace wasu jama’a sun jigata sakamakon wannan harbeharben.

Majiyar tace tawagar hadin guiwa ta ‘yan sanda da sojoji sun koma yankin Isoufia saboda lamurran ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamnan PDP na Borno Ya Fallasa Yadda Harin da Aka Kaiwa Tawagar Atiku Ya Faru

Yan ta’adda ba zasu tsorata jamia’an tsaro ba

Kamar yadda majiyar tace:

“Mambobin kungiyar miyagun sun yi tunanin zasu iya tsorata jami’an tsaron Anambra ta hanyar kai musu hari kullum.
“Suna tafka babban kuskure. Rundunar ‘yan sandan jihar tana da alhakin kare rayuka da kadarori kuma wannan harin ba zai tsayar dasu ba.”

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, sai dai ganau ya bayyana cewa ‘yan ta’addan suna amfani da motar alfarma kirar Venza SUV wacce yace sojoji sun kwace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng