Zaben 2023: Hukumar INEC Ta Mayar Da Martani Game Da Zargin Tinubu Safarar Miyagun Kwayoyi A Amurka

Zaben 2023: Hukumar INEC Ta Mayar Da Martani Game Da Zargin Tinubu Safarar Miyagun Kwayoyi A Amurka

  • Hukumar INEC ta yi martani kan wani rahoto da ya bazu da ke cewa tana bincikar Bola Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi da hadin gwiwar Amurka
  • INEC ta nesanta kanta daga wannan sanarwar tana mai cewa ba daga gare ta ya fito ba kuma babu gaskiya a cikinsa
  • Hukumar zaben ta yi kira ga al'umma su yi watsi da sanarwar da ta ce masu son kitsa makirci suka fitar, ta kuma shawarci su rika zuwa sahihin shafinta don samun bayani

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamba, ta yi martani kan rahoton cewa tana bincike kan zargin safarar miyagun kwayoyi kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, rahoton Vanguard.

A cikin wani sanarwa da hukumar ta fitar da Legit.ng ta gani, ta yi kira ga yan Najeriya su yi taka tsantsan da ikirarin cewa INEC na hadin gwiwa tare da gwamnatin Amurka don binciken zargin da ake yi wa Tinubu.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Bola Tinubu smiling
Zaben 2023: Hukumar INEC Ta Mayar Da Martani Game Da Zargin Tinubu Safarar Miyagun Kwayoyi A Amurka. Bpla Tinubu.
Asali: UGC

Ba mu binciken Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi - INEC

Hukumar ta ce wannan sanarwar da ya bazu ba daga INEC ya fito ba kuma hukumar zaben ba ta bincikar Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi, PM News ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Wata sanarwar manema labarai da aka ce hukumar ta fitar na ci gaba da bazuwa a intanet tun jiya Juma’a 11 ga watan Nuwamba 2022.
"Yana ikirarin cewa hukumar ta fara bincike kan batun kwace kadarori don laifi daga daya cikin yan takarar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe kuma tana hadin gwiwa da kotu a Amurka kan batun don duba yiwuwar saba dokokin zabe na 2022.
"Muna son fayyace cewa wannan sanarwar maneman labaran ba daga hukumar ta fito ba kuma ba ta wannan binciken. Aiki ne na masu makirci kuma rahoton bogi ne."

Kara karanta wannan

Karshen rikicin PDP: Wani tsohon shugaban kasa zai sulhunta Atiku da tawagar Wike

Muna shawartar al'umma su yi watsi da sanarwar - INEC

Da take bayyana sanarwar da aka ce ta yan jarida ne a matsayin karya, INEC ta bukaci yan Najeriya su rika ziyartar shafinta na intanet da shafukan sada zumunta don samun bayanai.

Ta kara da cewa:

"Ana shawartar al'umma su yi watsi da sanarwar manema labaran."

2023: Nasarar APC Na Cikin Haɗari, In Ji Shugaban Kamfen Na Adamawa

Sunny Sylvester Moniedafe, mataimakin direkta na kungiyoyin tallafi na kwamitin kamfen din yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC a Arewa maso Gabas, ya ce abin da wasu muhimman masu ruwa da tsaki a jam'iyyar a jihar Adamawa ke yi na barazana ga nasarar ta a zaben 2023.

Moniedafe, tsohon mai neman takarar shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana hakan ne yayin da ya tattauna da Daily Trust a ranar Alhamis a FCT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164