Likitoci Sun Cire Gurnet Da Ya Kusa Tashi Daga Kirjin Sojan Rasha

Likitoci Sun Cire Gurnet Da Ya Kusa Tashi Daga Kirjin Sojan Rasha

  • Likitoci a kasar Rasha sun ceci rayuwar wani soja mai yaki a bakin fama a yakin dake gudana a Ukraine
  • An bayyanawa Likitocin akwai yiwuwar bam din ya tashi yayinda suke tsakiyar gudanar da tiyatan
  • Sojan ya bayyana farin cikinsa bisa wannan tsallake rijiya da yayi da bayan kafa

Wasu Likitocin kasar Rasha cun samu nasarar cire gurnet mai iya tashi da ya makale a kirjin wani Sojan kasar.

Sojan mai suna Nikolay Pasenko, ya gamu da gurnet a faggen yaki a kasar Ukraine.

Tun watan Febrairu, gwamnatin Rasha ta fara yaki da Ukraine.

Glenn
Likitoci Sun Cire Gurnet Da Ya Kusa Tashi Daga Kirjin Sojan Rasha Hoto: @ZVEZDANEWS
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar DailyMail UK, Likitocin sun sanya rigar karfe gudun kada 'gurnet' din ya tashi da su suna tsakiyar aikin tiyata.

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

Pasenko da farko ya nuna rashin amincewarsa da aikin Tiyatan gudun kada ta tashi da Likitocin.

Daya daga cikin Likitocin yace:

"Makamin ya tsaya ne tsakanin 'aorta da 'vena cava' na kirjinsa. Ba sauki cire bam daga jikin mutum ba, saboda kokarin dauke abin daga dama zuwa hagu na iya kashe mara lafiyan."
"Yayinda muka samu nasarar cireta kuma aka sanya cikin kasa, kowa yayi murmushi."

Bayan aikin Tiyatan, Pasenko yace:

"Ni ban fahimci abin da ya faru ba. Wani abu ya bugi rigar yaki na kuma shikenan. Ko suma ban yi ba - haka na cigaba da tafiya na."

Ma'aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da aukuwan lamarin ranar Alhamis.

Rasha da Ukraine sun yi Yarjejeniya tsagaita wuta don Fitar da Kayan Hatsi

Bayan watanni ana fafatawa da yanke katse hanyoyin fitar d akayan abinci, Rasha da Ukraine sun yi yarjejeniya kan fitar da kayan hatsi.

Biyo bayan hauhawar farashin kayan hatsi a fadin duniya, da yiwuwan a samu saukin farashin kayan masarufi.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Kasar Rasha da Ukraine sun rattafa hannun kan sabuwar yarjejniya da kasar Turkiyya da Majalisar dinkin duniya kan fitar da kayan hatsi da ake bukata a fadin duniya.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa an yi wannan yarjejeniya ne ranar Juma'a.

Wannan yarjejeniya zai baiwa kasar Ukraine damar fitar da kayan hatsi sauran kasashen duniya tun bayan hanasu da Sojoji Rasha suka yi.

Ministan tsaron Rasha, Sergei Shoigu da Ministan ayyukan Ukraine Oleksandr Kubrakov, sun rattafa hannu kan yarjejeniyar lokuta daban-daban da Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres da Ministan tsaron Turkiyya, Hulusi Akar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel