Gwamnatin Najeriya Ta Sake Maka Nnamdi Kanu A Kotu, Ta Gabatar Da 'Sabbin' Tuhume-Tuhume 7

Gwamnatin Najeriya Ta Sake Maka Nnamdi Kanu A Kotu, Ta Gabatar Da 'Sabbin' Tuhume-Tuhume 7

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake gurfanar da tsararren shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, kan wasu sabbin tuhume-tuhume 7
  • A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015, ta nuna cewa gwamnatin tarayyar ta shigar da karar a babban kotun tarayya da ke Abuja kan wasu tuhume-tuhume 7 da ta yi wa kwaskwarima
  • A karar, FG ta yi zargin Kanu, wanda ke hannun DSS, ya wallafa sako da ke cewa duk wanda ya saba dokar zama a gida a kudu ya bar wasiyarsa

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake shigar da kara kan tuhume-tuhume bakwai da ta yi wa gyara kan Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar msu neman kafa Biyafra, IPOB da ke tsare.

Binciken da Vanguard ta yi ya nuna cewa karar da aka yi wa kwaskwarima mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015, wanda aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja na dauke da tuhume-tuhumen da a baya kotun ta amince da su.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Nnamdi Kanu
FG Ta Sake Maka Nnamadi Kanu A Kotu, Ta Gabatar Da Tuhume-Tuhume 7. Hoto: @VanguardNGR.
Asali: Twitter

Halin da ake ciki yanzu kan Nnamdi Kanu da IPOB

FG, din ta ce Nnamdi Kanu, wanda a halin yanzu ya ke tsare hannun DSS, a yayin da ya ke mamba na haramtaciyyar kungiya, ya yi barazana ga rayuwur duk wani wanda ya saba dokar 'zaman gida dole' a kudu maso gabashin kasar a sakon da ya wallafa yana mai cewa duk wanda ya saba dokar ya rubuta wasiyyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta fada wa kotu cewa sakamakon wannan barazanar; Bankuna, Makarantu, Kasuwanni, Kantina da gidajen man fetur da ke jihohin kudancin Najeriya sun cigaba da rufe kasuwancinsu, tare da hana mutane zirga-zirga, Vanguard ta rahoto.

FG ta kara da cewa shugaban na IPOB da ranaku daban-daban daga 2018 zuwa 2021, ya yi jawabi kuma an ji a Najeriya, yana harzuka mutane su yi farautan jami'an tsaron Najeriya su kashe su da iyalansu, wanda hakan laifi ne karkashin sashi na 1 (2) (h) na dokar kare ta'addanci na 2013.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Jingine Hukuncin Ɗaure Shugaban Hukumar EFCC Kan Saɓa Umurninta

Kazalika, ta yi zargin cewa Kanu ya umurci mambobin IPOB 'su kera bama-bamai", kana wanda aka yi karar, tsakanin Maris da Afrilun 2015, "ya shigo da na'urar watsa labarai mai suna Tram 50L ya ajiye a Ubulisiuzor a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra wanda ya bayyana a matsayin kayan gida, hakan kuma laifi ne da ya ci karo da shi na 47 (2) (a) na Criminal Code Act Cap, C45 na tarayyar Najeriya ta 2004".

Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya ce shi ba dan IPOB ba ne, bai ma da alaka da ita

Lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya Shuaibu Labaran Magaji ya bayyana cewa Nnamdi Kanu ya musanta cewa shi dan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ne a kotu ranar Laraba.

Magaji ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar kotun bayan an dage shari’ar Kanu zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164