Magidanci Ya Nemi Kotu Ta Raba Shi Da Matarsa Saboda 'Ɓarnatar Da Abinci'
- Wani magidanci da ke zaune a babban birnin tarayya Abuja ya garzaya kotu yana neman a raba aurensa da matarsa
- Mr Justine Onu, ya shaidawa kotu cewa matarsa, Joyce, bata iya tattalin abinci ba, kuma tana bin maza kana bata kula da yaransu
- A bangarenta, Joyce ta musanta dukkan wadannan zargin da Justine ya yi mata, kotu kuma ta dage cigaba da shari'a zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba
FCT, Abuja - Wani dan kasuwa, Mr Justine Onu, a ranar Alhamis, ya bukaci wata kotun kwastomari a Jikwoyi, Abuja, ta raba aurensa da matarsa, Joyce, yana zargin ta cika barna da almubazaranci.
Wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa matarsa bata san yadda ake lalaba abubuwa a gida ba, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
"Matata ba ta san yadda abubuwa suke wuya a kasa ba. Duk lokacin da za ta yi girki, ta kan dafa fiye da kima kuma daga baya a zubar a bola."
Mai shigar da karar ya kuma fada kotu cewa matarsa tana bin wasu mazaje kuma ya gaji da auren.
Onu ya sanar da kotu cewa ya kamu da ciwon hawan jini saboda zargin bin mazaje da ya ce matarsa na yi.
Nation Accord ta rahoto cewa ya kara da zargin matarsa ba ta da da'a kuma bata kulawa da yaransu.
Martanin matar
A bangarenta, Joyce, wacce aka yi kara ta musanta dukkan zargin da aka mata.
Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba.
Matata ta hana ni kusantar shimfidarta har duka na ta ke yi, Maigida ya fada wa kotu
A wani rahoton, wata kotun kwastamari a Ibadan, ranar Talata, ta raba auren shekara 11 tsakanin Nurudeen Mabinouri da Zainab kan rashin jima'i da tsoron kamuwa da cuttukan da ke yaduwa ta hanyar jima'in.
Da ya ke yanke hukunci, Chief Henry Agbaje, alkalin kotun yace "kotun tayi duk mai yiwuwa don ganin ta sasanta matsalar da ke tsakanin Mabinouri da Zainab sai dai abin ya ci tura".
Agbaje ya raba auren ne saboda shine maslaha kuma ya mika dan da yake tsakanin su ga Zainab din, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Asali: Legit.ng