Matata ta hana ni kusantar shimfidarta har duka na ta ke yi - Miji ya fadawa kotu

Matata ta hana ni kusantar shimfidarta har duka na ta ke yi - Miji ya fadawa kotu

- Alkalin da ya raba auren ya ce kotu tayi iya bakin kokarinta domin ayi sulhu amma abin bai yi wu ba

- Mijin ya yi ikirarin cewa matar tasa bata kwanciya da shi kuma tana dukansa ta kwace masa abubuwan da ya mallaka

- Matar tayi ikirarin cewa bin mata yake, ita kuma tana tsoron kada ta dauki cuta dalilin da yake hana ta kwanciyar dashi

Wata kotun gargajiya a Ibadan, ranar Talata, ta raba auren shekara 11 tsakanin Nurudeen Mabinouri da Zainab saboda rashin jima'i da tsoron kamuwa da cuttukan da ke yaduwa ta hanyar jima'in.

Da ya ke yanke hukunci, Cif Henry Agbaje, shugaban kotun ya ce "kotun tayi duk mai yiwuwa don ganin ta sasanta matsalar da ke tsakanin Mabinouri da Zainab sai dai abin ya ci tura".

Matata ta hana kusantar shimfidar ta har duka ta ke min
Matata ta hana kusantar shimfidar ta har duka ta ke min. Hoto: @TheNationNg
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su 'ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

The Nation ta ruwaito cewa Agbaje ya raba auren ne saboda shine maslaha kuma ya mika dan da yake tsakanin su ga Zainab din.

Sannan umarci Mabinouri da ya biya Naira 5,000 a matsayin kudin ciyar da dan duk wata.

Ya kuma yi umarnin da ya biya Naira 84,000 a matsayin kudin hayar Zainab da jaririnsu.

Da farko, Mabinouri ne yace bashi da sha'awar ci gaba da zama da matar saboda fitinar matar da rashin son zaman lafiyar ta.

"Fitinanniya ce, har duka na take tana kwace min abubuwa. Tana hana ni hakkin kwanciya," a cewarsa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar Muhammad Adahama

Da take maida martani, Zainab, ta bukaci Mabinouri da ya fadawa kotu gaskiya.

"Miji na yana dauke da cutar da zata iya yaduwa ta hanyar jima'i. Ina kauracewa kwanciya dashi saboda tsoron daukar cutar.

"Bin Mata yake. Yaki zuwa a duba shi ni kuma bazan sa rayuwata cikin hadari ba saboda shi," a cewarta.

Zainab ta ce iyayen Sa sun san dalilin da yasa take fatan ya sake ta.

A wani labarin daban, fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi - Lafia kan abinda suka kira 'batar mazakutar' mutum shida cikin wata guda a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164