An Gurfanar Da Wani Darakta da Ma'aikatan Gwamnati Kan Dukan Wani Alkalin Kotu

An Gurfanar Da Wani Darakta da Ma'aikatan Gwamnati Kan Dukan Wani Alkalin Kotu

  • Laifin Dukkan Ma'aikacin kotu a Nigeria yana daga cikin laifuka masfi muni da suke da hukunci mai tsauri
  • A Nigeria ana zargin ma'akatan Kotu da karbar na-goro dan shegawa mai kara ko wanda ake kara gaba
  • A satin nan ne shugaban Alkalan Nigeria ya rantsar da Sabbin alkalan da zasu saurari karar zaben shekarar 2023

Birnin-Kebbi: Wata kotun majastiri dake zamanta a baban birnin Jihar kebbi, Birnin-kebbi, ta gabatar da wani babban darakta a hukumar ilimin mai ta jihar, Aliyu Shehu Jega da wasu mutum biyu kan zargin dukan Alkalin kotu.

Wandanda dai ake zargin sun bayyana a gaban kuliya, su uku domin amsa laifin hada baki, tare da dukkan ma'aikacin kotu.

Kutun Majastari
An Gurfanar Da Wani Darakta da Ma'aikatan Gwamnati kan Dukan Wani Rijistaran Kotu Hoto: Jaridar Daily Trust
Asali: UGC

Yayin da mai gabatar da kara ke bayani yace "wanda ake zargin, yan sanda ne suka kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu kan dukan Alkalin kotun majastirin.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai gabatar da kara Dan Sanda Jubril Abba yace suna bukatar kotu ta basu dama dan ganin sun kara kimtsawa tare da gabatar da shaidu a gabanta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mai shigar da karar yace ana zargin masu laifin ne da hukuncin sabawa doka, taka hukuncin kotu da kuma laifin cin zarafi

Yace abinda ya faru shine:

lokacin da alkalin kotun yaje babbar ma'aikatar ilimi ta jiha a birnin kebbi, ya je zai yi alwala sai aka samu sabani da shi da daraktan wanda ta janyo ce-ce kuce wanda daga bisani ta sa daraktan marinsa baya da wasu mutum biyu da suka tayashi wajen dukansa.
Yace wanda aka daka din yana matakin na 16 na a aikin gwamnati, kuma shine Alkalin kotun majastiri mai mataki ta uku, indai za'ai masa haka to ina muka dosa.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Yace wannan ne shine lokaci na farko da aka taba ji ko gani yadda aka daki wani Alkalin kotu. kuma a kwanan ma ga yadda aka kashe wani alkali a gidansa. Ina ake so wannan abun ya tsaya?

Bayan ji ta bakin wanda suka shigar da karar Mai-Shari'a Hassan Kwaidijo ya daga shari'ar zuwa 28 ga watan nuwanban wannan shekarar.

An Kashe wani Alkali A Jihar Kebbi

A watan Agustan da ya wuce ne Rundunar yan sandan jihar kebbi ta tabbatar da kashe Mai Shari'a Attahiru Ibrahim dake unguwar Alieru a Birnin-Kebbi.

A cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ya fitar fitar tayi nuni da cewa "da misalin karfe tara na dare na ranar 25/08/22 suka samu labarin abinda ya auku a gidan mai shari'ar in suka kai masa dauki".

Yan Sandan jihar dai sun zargi matar marigayyin da hada hannu wajen kashe maigidan nata kamar yadda rahoton Radio Nigeria Kaduna ta wallafa.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel