'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah
- ‘Yan bindiga sun kai kazamin hari yankin Kaffinkoro a karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja
- Maharan sun yi ta harbi kan mai uwa da wahabi inda suka kashe mutum biyu inda harsashgi ya samu a kalla mutum 20
- Da yake tabbatar da lamarin, kwamishinan tsaro na jihar, Emmanuel Umar, ya ce gwamnati da hukumomin tsaro suna kan lamarin don dawo da zaman lafiya
Niger - Tsagerun ‘yan bindiga sun farmaki garin Kaffinkoro da ke karamar hukumar Paikoro a jihar Neja inda suka kashe wasu mutane biyu.
An tattaro cewa harbin bindiya ya samu a kalla mutane 20 baya ga wadanda suka mutu yayin da aka fatattaki mazauna yankin.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ‘yan bindigar sun farmaki garin da rana tsaka a kan babura kuma wani babur na dauke da a kalla mutane uku da muggan makamai.
Shigar ‘yan bindiga yankin ya haddasa rudani da tsoro yayin da suka fara harbi kan mai uwa da wahabi kuma hakan yasa mutane gudun neman tsira da rayuwarsu, rahoton Thisday.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata majiya ta ce ta sun hangi gawarwaki a kasa yayin da harbin bindiga ya samu a kalla mutum 20.
A cewarsa:
“Garin ya kusa zama kufai domin mutane sun shiga yar buya.”
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, babu tsaro a kasa domin ofishin yan sanda a garin ma ya zama babu kowa.
Kwamishinan tsaro na jihar Neja ya yi martani
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin agaji na jihar, Mista Emmanuel Umar, ya tabbatar da harin yana mai cewa gwamnati da jami’an tsaro suna kan lamarin.
Kwamishinan ya ce:
“Muna kan magance lamarin kuma ina mai baku tabbacin cewa ba da dadewa ba zaman lafiya zai dawo yankin.”
'Yan bindiga sun halaka mafarauta 5 a jihar Neja
Idan za a tuna, yan bindiga sun kashe mafarauta biyar a Garin Gabas da ke karamar hukumar Rafi ta jihar sannan suka sace wasu mutane a farkon watan nan.
Maharan dai sun isa yankin ne a kan babura sannan suka toshe hanya tare da tsare matafiya.
Hakazalika, ‘yan bindiga takwas da yan banga shida sun rasa rayukansu a yayin musayar wuta a kauyen Kundu da ke kusa da Zungeru a karamar hukumar Wushishi ta jihar a ranar Talata.
Asali: Legit.ng