Yanzu Yanzu: Yan Baranda Sun Cinnawa Ofishin INEC wuta a Wata Jihar Kudu Maso Yamma

Yanzu Yanzu: Yan Baranda Sun Cinnawa Ofishin INEC wuta a Wata Jihar Kudu Maso Yamma

  • Hukumar INEC ta tabbatar da harin da wasu yan baranda suka kai ofishinta na Iyana Mortuary a Abeokuta da ke jihar Ogun
  • Mai gadin ofishin na INEC ya kira yan sanda da tsakar dare don sanar da su batun harin kuma nan take suka garzaya wajen
  • Wadanda suka aikata ta'asar sun jika biredi a man fetur sannan suka dungi jefa shi cikin cibiyar ta baya

Ogun - Wasu yan baranda sun cinnawa ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a Iyana Mortuary da ke garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun wuta.

New Telegraph ta rahoto cewa yan barandan sun kai farmakin ne a tsakar daren Laraba, 9 ga watan Nuwamba sannan suka haura Katanga suka shiga harabar sannan suka cinna wuta ta baya.

Ofishin INEC da gobara ta ci
Yanzu Yanzu: Yan Baranda Sun Cinnawa Ofishin INEC wuta a Wata Jihar Kudu Maso Yamma Hoto: INEC
Asali: Twitter

Yadda yan barandan suka farmaki ofishin INEC a jihar Ogun

Kara karanta wannan

Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Arewa Ya Ba Da Hutun Kwana Daya

An tattaro cewa tsagerun sun jika biredi da man fetur sannan suka dungi jefa su cikin ginin ta bangarori daban-daban don kona ofishin na INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mai tsaron ofishin, Azeez Hamzat, ya yiwa yan sanda kiran gaggawa da misalin karfe 1:00 na tsakar dare, yana mai cewa cibiyar na ci da wuta.

Da suke amsa kira, an tura jami’an yan sanda daga sashin Ibara zuwa yankin, yayin da aka kira yan kwana-kwana, wadanda suka gaggauta zuwa wajen don kashe gobarar.

Annobar ta shafi dakin ajiyar kayayyaki, ofishin jami’an rijista da dakin taro.

Wata majiya ta kuma bayyana cewa gobarar ta kuma shafi wasu kayayyakin zabe.

Majiyar ta ce:

"Ba a rasa rai ba kuma babu wanda ya jikkata a gobarar."

INEC ta yi martani kan harin da aka kai ofishinta

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Bukaci N40m Kan Yara 20 Da Aka Sace A Neja

Da yake tabbatar da lamarin, kwamishinan zabe na jihar Ogun, Niyi Ijalaye, ya bayyana abun a matsayin mai ban al'ajabi.

Ijalaye ya ce:

"Da gaske ne cewa an cinnawa ofishinmu wuta. Yan sanda na bincike. Ban san mai zan ce ba. Ni kaina na kadu. Mun kira yan sanda da sauran hukumomin tsaro da daddare. Yan kwana-kwana sun daidaita lamarin. Har yanzu ana duba barnar da aka yi.
"Hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu. Za mu sake ganawa a yau don kawo wasu dabaru kan tsaron cibiyoyinmu."

Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng