Bayani: Ainihin Dalilin Da Yasa Kotu Ta Yanke Wa Shugaban EFCC Hukunci, Ta Tura Shi Gidan Yarin Kuje

Bayani: Ainihin Dalilin Da Yasa Kotu Ta Yanke Wa Shugaban EFCC Hukunci, Ta Tura Shi Gidan Yarin Kuje

  • A ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba, wata kotu a Abuja ta yanke hukunci kan shugaban hukumar EFCC
  • Mai shari'a Chizoba Oji ya ce ya tura Abdulrasheed Bawa gidan yari ne saboda kin bin umurnin kotu a baya
  • A wani sabon cigaba, shugaban na EFCC ya bayyana cewa ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke na tsare shi a Kuje

Kotu ta yanke hukuncin tura shugaban hukumar yaki da rashawa na EFCC, Abdulrasheed Bawa, gidan yarin Kuje saboda saba umurnin kotu.

Babban kotun tarayya a Abuja a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba, ta yanke wa Bawa hukunci, saboda saba umurnin kotu da ya danganci rashin aiwatar da umurnin kotu a baya.

Shugaban EFCC Bawa
Bayani: Ainihin Dalilin Da Yasa Kotu Ta Yanke Wa Shugaban EFCC Hukunci, Ta Tura Shi Gidan Yarin Kuje. Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta dura Jigawa, ta kama wani babban na hannun daman gwamna

A ranar Talata ne dai aka yanke wa shugaban na EFCC hukunci dangane da gazawar hukumar yaki da rashawar na kin bin umarnin kotu a baya.

Ta bada umurnin a kai Bawa gidan yari na Kuje da ke Abuja saboda saba umurnin kotu, a cigaba da tsare shi har sai ya wanke kansa daga laifin.

Bisa hakan ne, Legit.ng ta duba dalilin da ya sa kotun ta dauki matakin da kuma dalilin da ya sa kotun ta tura Bawa gidan yarin Kuje.

Saba umurnin kotu

Kotun ta umurci EFCC ta mayarwa tsohon direktan ayyuka na Rundunar sojojin saman Najeriya, NAF, Air Vice Marshall (AVM) Rufus Adeniyi Ojuawo, motarsa kirar Range Rover, da Naira miliyan 40.

EFCC ta gurfanar da Ojuawo kan tuhuma aikata laifuka biyu a gaban mai sharia Muawiyah Baba Idris na babban kotun tarayya a Abuja a 2016, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu Ta Bada Umurnin A Jefa Shugaban EFCC, Rashid Bawa, Gidan Yari

An zarge shi da karbar Naira miliyan 40 da Range Rover daga wani kamfani mai suna Hima Aboubakar of Societe D’Equipment Internationaux Nigeria Limited.

Amma, Ojuawo, a karar da lauyansa R.N. Ojabo, ya yi korafi cewa EFCC ta ki bin umurnin mayarsa da kadarorinsa da kotun ta yanke a hukuncin ranar 21 ga watan Nuwamban 2018.

Mai shari'a Chizoba Oji a ranar Talata, yayin hukuncinta ta ce shugaban na EFCC ya saba umurnin kotu kan shari'ar.

Mai shari'a ta ce:

"Shugaban Hukumar Yaki da Rashawar ya saba umurnin da wannan kotun ta bayar a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018 inda ta umurci hukumar ta EFCC, Abuja ta mayar wa wanda ya shigar da kara Range Rover dinsa (Super Charge) da kudi N40,000,000.00 (Naira Miliyan Arba'in)."

IGP Baba ya aiwatar da umurnin nan take, in ji kotu

Mai shari'a Oji bayan hukuncin na ranar Talata ta umurci sufeta janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba ya tabbatar an aiwatar da umurnin kotu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ASUU ta magantu kan za ta fara sabon yajin aiki ko kuma za ta ci gaba da aiki

Alkaliyar ta ce:

"Sifeta Janar na yan sandan Najeriya ya tabbatar cewa an aiwatar da umurnin wannan kotun."

Kotu ta ki amincewa a uzurin Bawa

Kotu ta ki amincewa da bayanin da lauyan EFCC, Francis Jirbo ya yi game da matakin da wanda ya ke karewa ya dauka.

Hukuncin da aka yanke a ranar 28 ga watan Oktoba, na ainihi (CTC) wanda Channels Television ta gani, kan kara ne da Air Vice Marshal (AVM) Rufus Adeniyi Ojuawo, tsohon direktan ayyuka na Rundunar Sojojin Saman Najeriya, NAF, ya shigar.

A karar, Ojuawo ya koka cewa EFCC ta ki bin umurnin kotu, na mayar masa da kadarorinsa da aka kwace, a hukuncin da ta bada a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018.

Ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa.

A cewar EFCC, laifin ya saba wa sashi na 17(a) na dokar rashawa da abubuwa masu alaka da shi na 2000, da hukuncinsa ke sashi na 17(c) na dokar.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Mai sharia Idris ya ce EFCC ta gaza gabatar da Ms Aboubakar, wanda aka ce shaida ne mai muhimmanci, tana mai cewa hakan zai iya janyo rasa rai.

Ya kara da cewa masu shigar da kara ba su yi kara kan Ms Aboubakar ba, wanda aka yi zargin ta bada N40 miliyan don alfarma.

Don haka, ya ce saboda rashin gabatar da Ms Aboubakar, masu shigar da karar sun gaza tabbatar da tuhumomi biyun da suke wa Mr Ojuawo.

Yayin watsi da karar, alkalin bada umurnin a mayarwa wanda aka yi karar motarsa Range Rover kuma a biya shi Naira miliyan 40.

Martanin shugaban EFCC

Saba Umurni: Mun daukaka kara, In Ji Bawa

Da ya ke martani kan batun, Abdularasheed Bawa, ya bayyana cewa ya daukaka kara kan hukuncin kotun.

Bawa ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya ke amsa tambayoyi daga yan jarida a Abuja.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

"Mun riga mun daukaka kara kan hukuncin don haka za mu bar doka ta yi aikinta."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164