Dan Najeriya Ya Ba da Labarin Rikicinsa da Bankin Zenith, Hakan Yasa Bai Samu Aiki a Bankin Ba
- Wani dan Najeriya ya shiga jimami yayin da ya bayyana tattaunawar neman aikin da ya yi da bankin Zenith bayan shekaru biyu da ya yada rubutu a Twitter game da bankin
- Mutumin ya ce yana gab da fara tattaunawar da sashen diban ma'aikatan bankin sai kwatsam wata mata ta shigo ta nuna masa abin da ya taba rubutawa game da bankin
- Jama'ar soshiyal midiya sun shawarci jama'a kan sakin baki a Twitter, tare da cewa hakan zai iya tsoma mutum cikin matsala
Wani ma'abocin shafin sada zumunta, @djbantiben1 ya bayyana yadda ya kaya da bankin Zenith lokacin da ya nemi aiki a bankin aka hanashi saboda ya taba maganar da bata dace ba a Twitter.
Rubutun na Twitter da ya taba yi a 2020 ne ya zama masa sanadiyyar rasa samun aiki mai gwabi a bankin.
Mutumin dai ya sake dawowa Twitter domin bayyana jimaminsa da abin da ya faru, ya ce ya yi kuka kamar karamin yaro.
Rubutun da ya yi har ya tunzura ankin
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya rubuta cewa:
"Na je tattaunawar neman aiki a makon da ya gabata a bankin Zenith. Wata mata daga HR ta shigo ta nuna min rubutu na na Twitter tun na 2020."
Ya kuma ambato rubutun da ya yi a baya, inda ya kira Zenith da lusarin banki a nahiyar Afrika. A cewarsa, a yanzu dai ya koyi darasi mai amfani.
'Yan Najeriya da dama kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu game da abin da ya faru dashi, inda suka ce hakan na faruwa, domin ana bincike kafin daukar mutum aiki.
Wasu kuwa suna kan ra'ayin cewa, mutum ba zai ki bayyana gaskiyar abin da yake ji ba don kawai tsoron me zai biyo baya na daukar aiki ko makamancin haka.
Yadda wata mata ta haukacewa banki saboda an cire kudinta
Ba sabon abu bane a Najeriya a samu tsaiko tsakanin banki da kwastoma.
A baya mun kawo muku rahoton yadda wata mata ta haukacewa banki saboda ganin an cire mata wasu adadi na kudadenta.
Fusatar da matar ta yi ya sa ta yi ikrarin yin tsirara a bankin saboda a cewarta, an cire mata kudi N100,000 ba tare da wani dalili ba.
Bidiyo dai ya nuna lokacin da matar ke kan ganiyar fushi, ta bayyana abin da ke ranta.
Asali: Legit.ng