Mu ba Ma’aikatan Wucin-gadi Bane: Shugaban ASUU ya Wanke FG Tas

Mu ba Ma’aikatan Wucin-gadi Bane: Shugaban ASUU ya Wanke FG Tas

  • ASUU ta bayyanawa gwamnatin tarayya cewa malaman jami’o’i ba ma’aikatan wucin- gadi bane don haka basu cancanci albashin rabin wata ba
  • Farfesa Osodeke ya sanar da cewa abinda gwamnatin tarayya tayi wa malaman ya take dokar daukarsu aiki da aka yi matsayinsu na malamai
  • Ya sanar da cewa malaman makarantar masu tunani na, kaifin basira da kuma kishin kasa kuma suna kira ga dalibai da iyaye da su fahimcesu

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, ASUU, ta caccaki gwamnatin tarayya kan biyan albashin rabin wata da tayi ga malaman a watan Oktoba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Half Salary
Mu ba Ma’aikatan Wucin-gadi Bane: Shugaban ASUU ya Wanke FG Tas. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta rahoto yadda aka biya malaman albashin rabin wata.

Gwamnatin tarayyan tayi bayanin cewa ta biya malaman albashi ne dogaro da kwanakin da suka yi suna aiki a watan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ASUU ta magantu kan za ta fara sabon yajin aiki ko kuma za ta ci gaba da aiki

Amma a yayin martani a ranar Talata, Emmanuel Osodeke, shugaban ASUU, yace mambobinsu ba ma’aikatan wucin-gadi bane kuma bai kamata a dinga yi musu tamkar irin wadannan ma’aikatan ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Osodeke ya kwatanta abinda gwamnatin tayi da karantsaye ga dokokin da aka dauke su aiki a kai, jaridar TheCable ta rahoto.

Yace majalisar zartarwa ta kungiyar sun bayyana mamakinsu kan yadda aka mayar da malaman tamkar ma’aikatan wucin-gadi wanda hakan bai taba faruwa ba a tarihin jami’o’i ba.

“Kungiyar ASUU ta janye yajin aikinta na tsawon wata takwas a ranar 14 ga watan Oktoban 2022 domin biyayya ga umarnin kotun masana’antu da kuma biyayya ga wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya kamar su kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.”

- Yace a wata takarda.

“Matakin da kungiyar ta dauka alama ce ta yarda da fannin shari’a kuma sauran cibiyoyi da rassan gwamnati da saka bukatar ‘yan kasa gaba da komai.

Kara karanta wannan

Albashin Rabin Wata: Majalisar Zartarwar ASUU ta Shiga Ganawar Sirri

“Wannan mun yarda a matsayinmu na masu tunani, fasaha da kishin kasa, ba wai zamu taimaka kawai wurin kwantar da tarzoma ba, amma zamu saka tabbatar da alaka mai kyau tsakanin gwamnati da ma’aikatan Najeriya baki daya.
“Sai dai kuma, martanin gwamnatin ga ASUU kan albashin da aka biya na kwanaki 18 na watan Oktoban 2022, ya ayyana mu a matsayin ma’aikatan da ake biya kullum.
“Wannan ba take doka bane kadai, wannan ya hada da karantsaye ga dukkan dokokin daukar aiki na malamai a dukkan duniya.”

Osodeke ya yabawa lakcarorin kan jajircewarsu tare da kira ga dalibai da iyayensu da su kasance masu fahimta yayin da ASUU ke kokarin sasanci tare da kiyaye doka.

Yace a taron gaggawar da majalisar zartarwa ta ASUU tayi a ranar Litinin, kungiyar ta zanta ne tare da tattaunawa kan dakatar da yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng