Kungiyar Malaman Jami’a Ta ASUU Ba Za Ta Sake Tsundumawa Sabon Yajin Aiki Ba
- Kungiyar malaman jami'a ta ce ba za ta kuma komawa sabon yajin aiki ba duk da gwamnati ta saba alkawarin da ta dauka musu
- Gwamnatin Najeriya ta biya ASUU albashin rabin wata bayan da ta janye yajin aikin watanni takwas da ta shiga a watan Fabrairu
- Kungiyar ta yi zama, ta kuma yi Allah-wadai da abin da gwamnatin Najeriya ta yi mata a makon da ya gabata
FCT, Abuja - Kungiyar malaman ta ASUU ta kammala zamanta na majalisar zartaswa, inda ta yanke ba za ta sake shiga wani sabon yajin aiki ba a nan kusa, Leadership ta ruwaito.
Sai dai, kungiyar ta yi Allah wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na son sake tunzura mambbointa ta hanyar biyansu rabin albashi na watan Agusta.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Talata bayan kammala zaman NEC, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, malaman jami'a masu ilimi ne ba wai ma'aikata gama gari ba.
Mun janye yajin aiki ne saboda 'yan Najeriya, inji ASUU
Ya kuma bayyana cewa, kungiyar ta janye yajin aiki a ranar 14 ga watan Oktoba ne bisa umarnin kotu da kuma yadda wasu 'yan Najeriya masu kishi suka sanya baki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga cikin wadanda suka sanya baki a lamarin dawowar ASUU bakin aiki akwai shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.
Osodeke ya kuma bayyana cewa, kungiyar ta nuna karimci wajen bin umarnin kotu da kuma sanya bukatun 'yan Najeriya a saman komai ta hanyar komawa bakin aiki.
A bangare guda, kungiyar ta nemi goyon bayan 'yan Najeriya a kokarinta na tabbatar da an warware dukkan wata dambarwa da ke tattare da yajin aikin na malaman jami'a, kamar yadda Punch ta ruwaito.
An biya malaman jami'a rabin albashin Oktoba
Idan baku manta ba, a baya gwamnati ta biya malaman jami'a albashin watan Oktoba, amma ba su iya samun cikakken albashin ba.
Kungiyar ta bayyana fushi yayin da mambobinta suka ga rabin albashin da suke samu sabanin cikakken kamar yadda suka saba.
Wannan ya biyo bayan janye yajin ne da kungiyar ta yi a tsakiyar wata, lamarin da yasa gwamnati ta ce ba za ta biya cikakken albashi ga ASUU ba.
Asali: Legit.ng