Tsohon Kakakin Gwamnan Jihar Neja, Ndayebo, Ya Rigamu Gidan Gaskiya
- Tsohon Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Neja, Malam Danladi Ndayebo, ya rasu ranar Litinin bayan hatsarin mota
- Mamacin, shugaban hukumar NIQS ta ƙasa ya rasa rasuwarsa ne sakamakon raunukan da ya ji a Hatsarin mota a Minna
- Tsohon Editan gidan jaridar Leadership, Ibrahim Sheme, ya kaɗu da jin labarin rasuwar tsohon abokin aikinsa
Minna, Niger - Shugaban hukumar Nigerian Institute of Quantity Surveyors, (NIQS), Danladi Ndyebo, ya rasu jiya Litinin sakamakon raunukan da ya samu a haɗarin mota ranar Lahadi da daddare.
Jaridar Daily Trust tace wani haɗarin Mota ya rutsa da Ndayabo tare da wani abokinsa, Muhammad Isa a Minna, babban birnin jihar Neja.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen biyu na kan hanyar zuwa Minna ne domin jajantawa abokinsu Alkali Aminu Garba, wanda ɗansa ya ɓata, sa'ilin hatsarin ya rutsa da su.
Daily Nigerian ta tattaro cewa a halin yanzun, wanda suka yi hatsarin tare, Muhammed na kwance ana kula da lafiyarsa a wani Asibitin Minna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tsakanin 2004 zuwa 2008, Marigayi Ɗanladi Ndayebo, ya yi aikin Edita daban-daban a jaridar Leadership, kana ya rike Darakta Janar na harkokin midiya da Sakataren watsa labarai ga tsohon gwamna, Babangida Aliyu.
Haka zalika mamacin ya rike kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja. Shugaban NIQS ya yi karatun Digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, kana ya yi Diplomar gaba da digiri kan aikin jarida duk a ABU.
'Mun yi Babban rashi'
A sakon ta'aziyyarsa, Tsohon Editan Leadership, Ibrahim Sheme, ya nuna kaɗuwa da samun labarin rasuwar Ndayebo.
"Allahu Akbar! Malam Danladi Ndayebo Editana ne mai kawo labarai lokacin ina aiki a jaridar Leadership. Rasuwarsa a wannan lokacin babban rashi ne gareni. Mutumin kirki ne na bugawa a jarida."
"Abokina ne har numfashinsa na ƙarshe. Rasuwar Ɗanladi babban rashi ne ba wai ga iyalansa kaɗai ba harda mu abokanansa. Ina rokon Allah mai rahama mara iyaka ya sa ya huta."
- Cewar Ibrahim Sheme a shafinsa na Facebook.
A wani labarin kuma Wutar Lantarki ta haddasa mummunar gobara a rukunin shagunan hukumar yan sanda da ke Lafiya, jihar Nasarawa
Rahoton da ya ishe mu daga bakin wani ganau ya nuna cewa wutar ta laƙume dukiyar yan kasuwa ta Miliyoyin naira da safiyar nan ta Talata.
A cewar wanda abun ya faru a idonsa, duk da zuwan jami'an kwana-kwana a kan lokaci, wutar bata lafa ba sai wajen karfe 7:00 na safe kuma ta fara ne tun 1:00 na dare.
Asali: Legit.ng