Kotun Jos Ta Yanke Wa Mai Gadi Hukuncin Daurin Watanni Shida Bisa Laifin Barci a Bakin Aiki

Kotun Jos Ta Yanke Wa Mai Gadi Hukuncin Daurin Watanni Shida Bisa Laifin Barci a Bakin Aiki

  • Kotun yanki a jihar Fikato ta yankewa wani mai gadi hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida
  • An zargi Abubakar Haruna da laifin sharba barci a lokacin da yake kan aikinsa na gadi a wani gida
  • Rahoton da 'yan sanda suka gabatar a gaban kotu ya bayyana gaskiyar abin da ya faru da kuma sassaucin da ya samu

Jos, jihar Filato - Wata kotun yanki a birnin Jos ta jihar Filato ta daure wani mai gadi, Abubakar Haruna a magarkama na tsawon watanni shida a ranar Litinin bisa kama shi da laifin sharbar barci a bakin aiki.

Rahoton da muka samo daga jaridar Vanguard ya ce, barcin da Abubakar ya yi ya kai ga shigowar barayi har suka saci karafan rodi da kwanon rufin gida.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Alkalan da suka yanke hukuncin, Malam Sadiq Adam da Mr Hyacenth Dolnanan sun yi hakan ne bayan da ya amsa laifinsa na yin sakaci da aikin da aka ba shi.

Sai dai, mai gadin ya nemi sassauki daga wurin alkali, inda aka bashi zabin biyan N10,000 a matsayin tara.

Yadda mai gadi ya sha dauri saboda barci a bakin aiki
Kotun Jos Ta Yanke Wa Mai Gadi Hukuncin Daurin Watanni Shida Bisa Laifin Barci a Bakin Aiki | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abubakar zai kuma biya N50,000 na diyya ga wanda ya shigar da karar, BBC Hausa ta tattaro.

Yadda lamarin ya faru

A tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Ibrahim Gowkat ya shaidawa kotun cewa, da fari wani Mr Adamu Isamail ne ya kawo batun Abubakar ofishin 'yan sanda na yankin Nassarawa Gwong a ranar 25 ga watan Agusta.

Ya bayyana cewa, Abubakar ya kasance mai gadi a gidan 'yar uwar Ismail.

Ya kuma shaida cewa, Abubakar ya sharbi barcinsa ne a lokacin da yake tsaka da aiki, lamarin da ya ba barayi damar shiga tare da sace janareta, bandir din kwano, da kuma rodi guda 25.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

Hakazalika, ya shaida cewa, laifinsa ya saba da sashe na 164 na kundin laifuka da hukunci na yankin Arewaacin Najeriya.

An Gurfanar Da Wani Magidanci A Kotu Kan Daba Wa Surukinsa Kwalbar Giya

A wani labarin, Tunde Odedo, wani magidanci mai shekaru 43 ya bayyana gaban kotun Majisteren Abeokuta bisa zargin ya caka ma surukinsa; mahaifin matarsa kwalbar giya a kai.

An tsare wannan magidanci ne har zuwa lokacin da ya cika ka'idar beli, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Odedo, wanda ake zargi da laifuka biyu da suka hada da hada kai wajen aikata barna da cin zarafi ya aikata laifin ne tare da wasu mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.