Gwamnatin Katsina Ta Haramta Amfani Da ’Yan Daba a Kamfen 2023

Gwamnatin Katsina Ta Haramta Amfani Da ’Yan Daba a Kamfen 2023

  • Gwamnan jihar Katsina ya ayyana dokar hana amfani da 'yan daba a zaben 2023 mai zuwa nan da badi
  • Ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawari kan harkokin tsaro, ya kuma ba 'yan siyasa shawari mai kyau
  • Gamayyar kungiyar farar hula ta yabawa gwamnan, ta kuma bayyana kwarin gwiwar samun zabe na gari a Katsina

Jihar Katsina - A kokarin tabbatar da zaben 2023 cikin aminci, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanya hannun kan dokar hana damawa da 'yan daba a gangamin zabe a fadin jiharsa, AIT ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin mai ba shi shawari kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina, kuma ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaban shugabannin da suka dace a zaben da za yi.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

Masari ya hana amfani da 'yan daba a zaben 2023 a jiharsa
Gwamnatin Katsina Ta Haramta Amfani Da ’Yan Daba a Kamfen 2023 | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, tunda wannan ne zaben karshe da za a yi a mulkin Masari, yana da kyau a yi shi cikin aminci domin kafa tarihi na gari a jihar.

Hakazalika, ya ce gwamna Masari dattijon kasa ne, kuma zai tabbatar da zaman lafiya a jihar, musamman a kokarinsa na dawo da martabar jihar a matsayin kasa mai tarbar baki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku dauki 'ya'yan talakawa kamar naku, Masari ga 'yan siyasa

Daga karshe ya shawarci 'yan siyasa da suke yiwa 'yan daba kallon 'ya'yansu kuma ya kamata su ba su wadataccen ilimi a madadin bata rayuwarsu ta hanyar mai dasu tsageru.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula ta CCSO, Abdulrahman Abdullahi ya yaba da kokarin Masari na damawa da 'yan daba, tare da bayyana cewa hakan zai tabbatar da zabe na gari a Katsina.

Kara karanta wannan

Tsaiko ga daliban Najeriya yayin da ASUU ke shirin komawa yajin aiki saboda dalili 1

Daga nan ne ya ce, idan gwamnati ta tabbatar da cikakken amfani da dokar, zai zama mafi alherin abin da gwamnan ya assasa.

Jaridar Vanguard a baya ta ruwaito yadda gwamnan ya yi irin wannan hani a watan Fabrairun 2022.

Akwai Yuwuwar ’Yan Siyasa Su Yi Amfani Da ’Yan Daba Wajen Gangamin Kamfen Zaben 2023, Inji DSS

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadin cewa, akwai yiwuwar 'yan siyasa a kasar nan su yi amfani da tsagerun 'yan daba a gangamin su na zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan DSS a Kaduna, Mr Abdul Enachie yayin gabatar da rahotonsa kan tsaro a jihar ta Kaduna.

Ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnati ta mai da hankali sosai tare da wayar da kan matasa don gudun amfani dasu wajen aikata barna a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Akwai rikici a kasa: DSS ta gano sirrin 'yan siyasa, za su yi amfani da 'yan daba a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.