Mata Ta Haifi Jariri a Cikin Jirgi, a Nisan Kafa 36,000 a Sararin Samaniya

Mata Ta Haifi Jariri a Cikin Jirgi, a Nisan Kafa 36,000 a Sararin Samaniya

  • Wata 'yar shekara 21 a kasar Amurka mai suna Kendria Rhoden ta haifi jaririnta a cikin wani jirgin da ya tashi a birnin New York
  • An ce Kendria na kan hanyarta ta zuwa jamhuriyar Dominican ne, kuma likitoci sun tantance ta kafin tashin jirgin
  • Ta haifi kyakkyawan jaririnta a nisan kafa 36,000 a sararin samaniya, don haka ta sanya masa suna Skylen

An haifi wani kyakkyawan yaro a nisan kafa 36,000 a sararin samaniya jim kadan bayan da mahaifiyarsa ta fara nakuda a cikin jirgi, CBS News ta ruwaito.

Mahaifiyar 'yar shekaru 21 mai suna Kendria Rhoden na kan hanyarta ta zuwa jamhuriyar Dominican ne a lokacin da lamarin ya faru.

Budurwa ta haihu a cikin jirgin sama
Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Dakin Kwanan Dalibai a Makarantar Tsangaya a Jihar Kano | Hoto: Caters News Agency
Asali: Facebook

Kendira dama ta dan dara wa'adin haihuwarta a daidai lokacin da ta hau jirin American Airlines daga birnin New York.

Kara karanta wannan

Tsohon Babba Sakatare a Wata Jiha Ya Yanki Jiki Ya Faɗi, Allah Ya Masa Rasuwa

Kwatsam Kendria ta fara nakuda a jirgi

Bayan da jirgin ya tashi, matar ta fara jin ciwon ciki, alamar ta fara jin kamar tana nakuda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tuni kawai ta sanarwa ahalinta da ke gefe a cikin jirgin cewa ta fara ganin nakuda.

Kendria ta shaida cewa:

"Haka dai ya ci gaba sannan bayan mintuna 34 da tashin jirgin, kawai ruwa ya balle mini. Ma'aikatan jirgin sun taimaka mini sosai."

'Yar uwarta, Kendalee ta yi martani da abin da ya faru, inda ta shaidawa New York Post cewa:

"Na razana. Sai da nai ta tambayarta ko ta tabbata nakuda ne har sai da ta tashi, sannan na ga gaba daya wurin zamanta ya jike."

Matar da ta haihun ta ce:

"An dauke ta zuwa bayan jirgin, sannan bayan mintuna 20 tana fama, aka sanar cewa an samu sabon fasinja a jirgin, kyakkyawan yaro mai suna Skylen.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Jirgin Sama Ɗauke da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Zarce Cikin Kogi

"Kawai ina tuna yadda mutane suka dinga daukar bidiyonmu yayin da muke sauka daga jirgin, kuma duk suna taya ni murna."

Budurwa Ta Yada Bidiyon Kalan Takalmin da Saurayinta Yazo Dashi Neman Aurenta

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya mai suna @black.teenah ta yada bidiyo mai ban dariya na wani manemin aurenta.

Kamar yadda ya bayyana, mutumin ya zo gidan su budurwar ne domin neman aurenta.

Yayin da ya cire takalminsa ya shiga gidan su Teenah, ta kadu bayan ganin irin takalmin da ya zo dashi.

Ta dauki bidiyonsa, kana ta yada shi a kafar TikTok, inda ta bayyana wani mataccen takalmi na mutumin da ke son aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel