Tsohon Babban Sakatare a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu

Tsohon Babban Sakatare a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu

  • Tsohon Babban Sakatare a ma'aikatar Ilimi ta jihar Bayelsa, Dakta Walton Liverpool ya yanke jiki ya faɗi matacce
  • Bayanai sun nuna cewa yana fama da ciwan hawan jini kuma ya rasa rayuwarsa ne a Asibitin UBTH jihar Edo lokacin da yaje harkokin kasuwanci
  • Wata majiya daga cikin iyalansa ta ce mata da 'ya'yan marigayin sun yi kokarin hana shi tafiyar amma ajali ya kira shi

Yanagoa, Bayelsa - Tsohon babban Sakatare a ma'aikatar Ilimi ta jihar Bayelsa, Dakta Walton Liverpool, ya yanki jiki ya faɗi kuma Allah ya masa rasuwa.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya auku ne a Asibitin koyarwa na jami'ar Benin (UBTH) da ke jihar Edo bayan rashin lafiyarsa ta yi tsanani, yayin da yaje harkokin kasuwanci jihar.

Taswirar jihar Bayelsa.
Tsohon Babban Sakatare a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Faɗi, Ya Mutu Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

An tattaro cewa Dakta Liverpool wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati, yana fama ne da lalurar hawan jini.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Yadda budurwa ta haifi jaririnta a jirgin sama mai nisan kafa 36,000 a sama

Wata majiya tace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An ce rashin lafiyarsa ce ta tashi bayan share tafiya har zuwa Patakwal, babban birnin jihar Ribas a kan babbar motar dakon kaya sakamakon ambaliyar ruwan da ta ɗaiɗaita Titin East-West."
"Kuma daga nan ya hau Jirgin sama zuwa jihar Legas duk da rashin lafiyar da yake fama da ita da kuma gargaɗi da yunkurin matarsa da 'ya'yansa na ya hakura da tafiyar nan."

Wata majiya mai kusanci da iyalansa ta bayyana cewa jikinsa ya ƙara tsananta lokacin da ya isa Edo bisa haka aka yi gaggawar kai shi Asibitin kuɗi domin kula da lafiyarsa.

Ta ƙara da cewa da abun ya sha ƙarfinsu suka umarci a wuce da shi Asibitin koyarwa na jami'ar Benin, Ondo, inda anan ne mai faruwa ta faru, rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

A wani labarin kuma Wani Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Afka Cikin Tafkin Victoria

Wani Jirgin sama ya yi hatsari inda ya afka cikin Kogin Victoria dake ƙasar Tanzaniya a yayin da yake kokarin sauka a Filin sauka da tashin jirgen sama na Bukoba Airport kusa da Kogin.

Hukumar watsa labarai ta ƙasar Tanzaniya (TBC) tace zuwa yanzun an samu nasarar ceto Fasinjoji 15 da haɗarin ya rutsa da su, kamar yadda jaridar Premium Tim es ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262