Matar mutum kabarinsa: Fasto ya auri budurwarsa mai shekara 63 bayan ta ki shi shekara 50 baya

Matar mutum kabarinsa: Fasto ya auri budurwarsa mai shekara 63 bayan ta ki shi shekara 50 baya

Hausawa sun yi gaskiya a Karin maganar nan suke yin a cewa matar mutum kabarinsa kuma in dai akwai rai toh akwai rabo, hakan ne ya kasance da wani Fasto da budurwarsa da ya so aure a shekaru 50 da suka shige amma ta ki amincewa dashi.

Sai gashi a ranar 29 ga watan Yuni, faston mai suna Mathew Owojaiye mai shekara 73 ya angonce da ita waccan tsohuwar budurwar tasa mai suna, Farfesa Abosede Igunnu, domin bata taba aure ba duk da cewar a yanzu tana da shekara 63.

Anyi bikin auren ne a cocin Living Faith da ke Dogarawa, karamar hukumar Sabon gari da ke jihar Kaduna, inda auren ya samu halartan dumbin jama’a da dama.

Matar dai ta kasance ma’aikaciya a kwalejin ilimi na tarayya da ke garin Zaria.

KU KARANTA KUMA: Wani jigon APC yayi cakacaka da Obasanjo, yace Buhari na iya bakin kokarinsa

An tattaro cewa angon Owojaiye ya taba neman Abosede don su yi aure kimanin shekara 50 da suka gabata, lokacin tana ’yar shekara 13 a duniya.

Amma a wancan lokaci ta ce ita makaranta za ta yi, don haka sai ya hakura. Daga bisani dai shi ya yi aurensa har ya hayayyafa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel