Yara 21 Da Yan Ta'adda Suka Sace A Jihar Katsina Sun Kubuta

Yara 21 Da Yan Ta'adda Suka Sace A Jihar Katsina Sun Kubuta

  • Yara 21 da aka sace a wata gona da ke kauyen Mairuwa a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina sun samu yanci
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Kakakin yan sandan bai yi magana kan cewa ko an biya fansa ba ko ba a biya ba kafin sakin yaran amma ya ce an sada su da yan uwansu kuma ana bincike

Jihar Katsina - Yara guda 21 da yan ta'adda suka sace a Jihar Katsina sun shaki iskar yanci, rahoton Channels Television.

An sace yaran ne a ranar Lahadi yayin da suke aiki a wani gona a garin Mairuwa, karamar hukumar Faskari.

Yanzu
Yara 21 Da Yan Ta'adda Suka Sace A Katsina Sun Kubuta
Asali: Original

Asusun Yara Na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, a ranar Juma'a ta bukaci hukumomi su tashi tsaye su ceto yaran.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Likitoci Sun Bayyana Abin Da Ya Haddasa Mutuwar Ɗan Davido, Ifeanyi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A sanarwar da wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms Cristian Munduate, UN din ta bayyana sace yaran a matsayin abin 'mara kyau'.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Sambo Isah ya tabbatar da sakinsu a wani sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Ya ce wadanda aka ceto din sun hada da mata 17 da maza hudu kuma tuni an sada su da yan uwansu yayin da ake cigaba da bincike.

Sanarwar ta ce:

"Barka da yamma yan jarida. Ina farin cikin sanar da sakin ma'aikata 21 da aka sace a gona a kauyen Kamfanin Mai Lafiya jihar Katsina. An sada su da yan uwansu. Ana cigaba da bincike."

Kakakin yan sandan bai fadi ko an biya kudin fansa ba ko ba a biya ba, Daily Trust ta rahoto.

A gefe guda, wata majiya daga garin wadanda aka sace din ta shaidawa Channels Television cewa yan ta'addan suna neman a biya su fansar Naira miliyan 30 ko basu daman yin magana kai tsaye da mai gonar da wadanda aka sace suke aiki a can.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Gobara Ta Kama Hedkwatar Hukumar NYSC Dake Birnin Tarayya Abuja

Majiyar ta ce:

"Yan ta'addan sun tuntubi wasu iyayen wadanda suka sace domin maganan kudin fansa. A cewarsu, ba za su karbi kasa da Naira miliyan 30 ba ko magana kai tsaye da mai gonar. Sun ce sunyi bincikensu sun gano cewa mai gonar yana da kudi sosai."

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164