'Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sanya Wa Manoma Haraji a Jihar Neja
- 'Yan bindiga na ci gaba da barazana ga wasu mazauna a jihar Neja, sun ce za su kakaba musu haraji nan gaba kadan
- An sace hakimin yankin Atabo a karamar hukumar Magama, amma daga baya an sako shi ba tare da fansa ba
- Yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar munanan hare-hare daga 'yan bindiga dadi
Jihar Neja - Manoman yankin Atabo da yankunan da ke zagaye da yankin a karamar hukumar Magama ta jihar Neja sun shiga firgici biyo bayan barazanar da 'yan bindiga ke yi na sanya musu haraji.
A cewar rahoton Daily Post, 'yan bindigan na kokarin sanya wannan haraji ne kafin ba manoma damar fara girbin amfanin gona na noman rani da suka yi.
An sace hakimin yankin Atabo
An tattaro cewa, 'yan bindiga sun mamaye yankin Atabo a ranar Talata, sun yi awon gaba da hakimin yankin, Alhaji Mairabo da wani kanensa da ake kira Usman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarjo cewa, daga baya an sako hakimin a ranar Laraba, sai dai an rike kanen nasa da aka sace su tare.
A cewarsa:
"Sun saki hakimin kauyen a ranar Laraba kuma sun shaidawa iyalan kanen nasa su biya kudin fansa Naira miliyan 7.
"Sun kuma shaida masa cewa, idan ba a biya wannan fansa ba a kan lokaci ba, ba za su bari a yi girbin amfanin noman rani ba har sai an biya haraji.
"Da nake magana da kai yanzu, mutane da yawa sun bar gidajensu saboda harin na ranar Talata."
Mazauna yankin sun bayyana neman agaji da ceto daga gwamnati da jami'an tsaro domin su samu damar tattara amfanin gonakinsu lafiya.
Sojoji Sun Kama Mutum 60 da Ke Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba a Abuja
A wani labarin, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a babban birnin tarayya Abuja, jami’an sojin Najeriya sun kai samame wani yankin hakar ma’adinai da ake haka ba bisa ka’ida ba.
An kai farmakin ne a yankin Tukashara Wasa, Apo a tsakiyar birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Wannan batu na zuwa ne ta bakin Manjo Janar Musa Danmadami, babban daraktan yada labarai na gidan tsaro a Najeriya.
Asali: Legit.ng