Jami’an NDLEA na Fuskantar Barazana da Kisa daga Dillalan Kwayoyi, Marwa

Jami’an NDLEA na Fuskantar Barazana da Kisa daga Dillalan Kwayoyi, Marwa

  • Birgediya janar Buba Marwa mai ritaya, shugaban Hukumar NDLEA yace manyan dillalan miyagun kwayoyi na halaka jami’anta dake zama a garuruwa da birane
  • Marwa wanda ya bayyana gaban majalisar tarayya domin kare kasafin kudin hukumar, yace bai dace su kasance cikin mutane ba, sun fi dacewa da bariki saboda hatsarin aikinsu
  • Marwa ya sanar da cewa suna bukatar makamai na zamani wadanda zasu ci galaba kan dillalai da masu safarar miyagun kwayoyi a kasar nan

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, Birgediya janar Buba Marwa mai ritaya, a ranar Lahadi yace manyan dillalan miyagun kwayoyi suna halaka jami’an hukumar duk a cikin matakin da suka dauka kan sabunta yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Buba Marwa
Jami’an NDLEA na Fuskantar Barazana da Kisa daga Dillalan Kwayoyi, Marwa. Hoto daga thenatinononlineng.net
Asali: UGC

Marwa ya sanar da hakan yayin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai domin kare kasafin kudin hukumar na 2023, jaridar The Nation ta rahoto .

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano

Baya ga haka, ya jaddada cewa Akwai bukatar samar da bariki domin jami’an hukumar.

“Batun samar da bariki yana da matukar amfani gare mu saboda mun san cewa NDLEA ta tashi tsaye kan masu safarar miyagun kwayoyi da dillalansu kuma idan aka kama su, aka gurfanar dasu tare da aikesu gidan yari basu jin dadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A don haka ne suke farautar jami’anmu kuma muna zama cikin birane. Ana samun wadanda ake lahantawa har da kashewa.”

- Yace.

Yace da amincewar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ana gina barikoki ta jami’an hukumar a karo na farko.

Yace hukumar na kan gina gidan horo uku, dakunan bincike biyu da kuma samar da kayayyakin tsaro.

Yace hukumar ta kammala tsarikan samun filaye a Adamawa, Abuja da Legas domin gina barikoki.

Marwa ya kara da cewa, akwai bukatar a inganta siyan karin makamai domin amfanin hukumar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace dan takarar majalisa na jihar Zamfara

“Akwai bukatar mu kasance da makaman zamani da zamu fi karfin masu safarar kwayoyin ballantana yayin da muke bin su har daji.”

- Yace.

Yace N24 biliyan aka warewa ayyukan gina barikokin a kasafin kudin 2022 amma an zabtare tare da mayar da shi N13 biliyan a kasafin kudin 2023.

Yayi kira kan cewa an kara musu N10 biliyan domin aiwatar da manyan ayyukan.

NDLEA Ta Kama Basaraken Arewa da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

A wani labari na daban, jami’an hukumar hana fatauci da shan miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama hakimin garin Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, Abubakar Ibrahim mai shekaru 38 kan fataucin kwayoyi.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, a Abuja, cewa an kama Ibrahim da ganyen wiwi mai nauyin kilo 3 da kuma kwayoyin exol-5 guda 4,000, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng