An Gurfanar Da Wani Magidanci A Kotu Kan Daba Wa Surukinsa Kwalbar Giya
- Wani magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya dabawa surukinsa kwalbar giya a kai a jihar Ogun
- Wannan lamari ya faru ne yayin da surukan suka zauna domin warware wata matsalar aure, lamari ya zama mara dadi
- Ana yawan samun tsalolin aure a Najeriya, har a kan zubar da jini a irin wadannan matsaloli da ke faruwa
Jihar Ogun - Tunde Odedo, wani magidanci mai shekaru 43 ya bayyana gaban kotun Majisteren Abeokuta bisa zargin ya caka ma surukinsa; mahaifin matarsa kwalbar giya a kai.
An tsare wannan magidanci ne har zuwa lokacin da ya cika ka'idar beli, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Mr Odedo, wanda ake zargi da laifuka biyu da suka hada da hada kai wajen aikata barna da cin zarafi ya aikata laifin ne tare da wasu mutane.
Mai shari'a O.A Akamo-Oyede ya ba da belin Odede, amma ya ce a ci gaba da tsare shi har sai ya kawo kudin belin da ya kai N50,000 tare da masu tsaya masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a ya dage sake sauraran karar har zuwa ranar 23 ga watan Nuwamban bana.
Yadda lamarin ya faru
A tun farko, jami'ar 'yar sanda mai gabatar da kara, sufeto Evelyn Motim ta shaidawa kotu cewa, Odedo ya aikata wannan laifin ne a ranan 30 ga watan Oktoba da misalin karfe 7:50 na yamma a yankin AbuIe Ijaye kusa da hanyar Ayetoro a Abeokuta.
Ta bayyana cewa, kwatsam bayan samun sabani, Odedo ya samu fasasshiyar kwalbar giya ta daba wa surukin nasa a ka.
Ta kara da cewa, an gayyaci Odedo ne ya zo don warware wata matsalar aure, amma ya hada baki da wasu kana ya dabawa surukin nasa kwalba, rahoton Aminiya.
Hakazalika, wasu daga surukan da ke wurin da lamarin ya faru sun samu raunuka da dama.
A bangaren doka, ta ce wadannan lafuka biyu na hada baki da farmakar suruki sun saba da sashe 516 da 355 na kundin manyan laifuka na jihar Ogun na shekarar 2006.
Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Uku a Jihar Anambra
A wani labarin, hadin gwiwar jami'an tsaro a jihar Anambra sun yi bata-kashi da wasu tsagerun 'yan bindiga, sun hallaka uku.
Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba a Umunze, karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar ta Anambra.
Rahoton da muke samo daga jaridar The Nation ya bayyana cewa, an samu layu da guraye a jikinsu, musamman a kafa, wuya, kugu da hannaye.
Asali: Legit.ng