Mummunar Ambaliya Ta Kori Sarki, Mai martaba Ya Koma Kwana Cikin Mota

Mummunar Ambaliya Ta Kori Sarki, Mai martaba Ya Koma Kwana Cikin Mota

  • Sarkin garin Tungbo a Karamar Hukumar Sagbama ya hakura da zaman fadarsa saboda ambliyar ruwa
  • Mai martaba Amos Poubinafa yace dolensa ya koma kwana a mota a dalilin ambaliyan ruwan da aka yi
  • Tsohon sojan yayi alwashin ba zai bar mutanensa saboda musibar da aka shiga ba, ya yi zamansa a Tungbo

Bayelsa - Basaraken da yake rike da kasar Tungbo a karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa, Cif Amos Poubinafa, ya samu mafaka a cikin motarsa.

Premium Times tace Mai martaba Amos Poubinafa ya dawo rayuwa a mota ne a dalilin ambaliyar ruwan da ta barke a Bayelsa da wasu jihohin Najeriya.

Sarkin na Tungbo yace ruwa ya kora sa daga fadarsa, hakan ta sa ya shafe kwanaki a Toyota Sienna.

“A cikin motata kirar Toyota Sienna nake kwana yanzu, tsawon makonni biyu tun da ambaliya ta shafe fadar.

Kara karanta wannan

Abin da ya Haddasa Fadanmu da Murtala Garo a gidan Gawuna - Alhassan Doguwa

Ruwan ya yi zurfi, yana shanye gwiwa, hakan ya yi sanadiyyar da ba za a iya rayuwa a cikin fadar Sarki ba.

- Amos Poubinafa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Iyalin Sarki sun yi gudun hijira

Basaraken ya shaidawa hukumar dillacin labarai cewa a duk fadarsa babu inda zai iya barci, dole ya koma motarsa, yayin da iyalinsa suka bar garin.

Mummunar Ambaliya
Ambaliya a Bayelsa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

The Cable ta rahoto Amos Poubinafa yana cewa ba zai iya barin kasarsa domin samun mafaka ba, musamman ganin horon da ya samu a gidan soja.

“Motar ce ta fi aminci a gare ni, ruwa ya shanye gaba daya ginin, babu wani wurin da zan iya barci hankali kwance.
Iyalina sun koma garin Yenagoa. A matsayin jagora (Sarkin gargajiya) na al’umma, ba zan bar talakawa, in tsere ba.
Saboda horaswan da aka yi a mani na sojan ruwa, ba a tunanin zan bar mutane na, zan kasance na karshe a nan."

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

- Amos Poubinafa

Mai martaba ya yi kira ga gwamnati

A rahoton da Aminiya ta fitar, an ji Sarkin yana kira ga gwamnatin tarayya ta gina madatsai, kuma a yashe kogin Neja da na Benuwai domin a daina ambaliya.

Wannan baya ga rokon da ya yi ga NEMA da hukumar bada agaji ta jihar Bayelsa da sauran masu abin hannu, da su taimakawa mutanen da ke garin Tungbo.

2023 sai Obi - Samuel Ortom

An ji labari Samuel Ortom yace ba don shi jam’iyyar PDP ba ne, da ya yi wa Peter Obi da Jam’iyyarsa ta LP aiki a zaben Shugaban kasa da za ayi a shekarar badi.

Ortom yace duk da irin cacantar Obi, iyakarsa da shi a zabe mai zuwa shi ne addu’a. Gwamnan ya bayyana haka da 'dan takaran ya kai masu ziyara a Makurdi.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Halaka Mahaifin Budurwarsa Mai Shekaru 68 a Bauchi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng