'Yan Ta'adda Sun Kashe Rayuka, Sun Tafka Mummunar Ta'asa a Sabon Harin Zamfara

'Yan Ta'adda Sun Kashe Rayuka, Sun Tafka Mummunar Ta'asa a Sabon Harin Zamfara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai harin ta'addanci kan mutane ana tsaka da cin kasuwa a jihar Zamfara
  • Wani mazaunin ƙauyen Gidan Goga da lamarin ya auku, yace mutum 2 sun mutu, maharan sun sace wasu kuma sun kona kasuwa
  • Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan Zamfara, SP Mohammed Shehu, bai ce uffan ba har zuwa lokacin haɗa rahoton

Zamfara - 'Yan ta'adda sun yi ajalin rayukan mutum biyu, sun yi awon gaba da wasu da dama kana suka kona kasuwar Gidan-Goga da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Wani ɗan asalin kauyen, Mohammed Musa, ya shaida wa wakilin jaridar Punch cewa yan ta'addan a kan Babura sun ƙona kasuwar ranar Laraba, sakamakon haka dukiyar miliyoyi ta salwanta.

Rashin tsaro a arewa.
'Yan Ta'adda Sun Kashe Rayuka, Sun Tafka Mummunar Ta'asa a Sabon Harin Zamfara Hoto: punchng
Asali: Twitter

"Sun kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da wasu bayin Allah da yawa yayin da wasu suka samu raunuka," inji Musa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Yan Gudun Hijra, Sun Kashe Mutum 4

Mutumin ya ƙara da cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yan ta'adda sun isa kasuwar lokacin da mutane ke hada-hadar kasuwanci, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi. Hakan ya ta da hankulan mutane suka fara turereniyar neman tsira sakamakon haka da yawa suka jikkata."
"Bayan haka ne yan bindigan suka cinna wa kasuwar wuta daga bisani suka tasa keyar mutanen da suka yi garkuwa da zuwa cikin jeji."

Musa ya bayyana cewa har yanzun ba'a gano adadin yawan mutanen da maharan suka sace ba saboda mafi yawa ba 'yan asalin ƙauyen bane.

"Mafi yawa sun zo cin kasuwa ne daga wurare daban-daban, bisa haka bamu iya tantance adadin da aka sace ba amma zasu haura 30."

Da ake nemi mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ta wayar salula ba'a same shi domin jin ta bakinsa har zuwa wannan lokacin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Sojoji da 'Yan Sanda Sun Sheƙe Hatsabiban Yan Bindiga Uku, An Gano Wani Abu a Jikinsu

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Kwamandan hukumar NSCDC, sun harbi Kaninsa

A wani labarin Yan bindiga sun sace matar Kwamandan sashen leken asiri na shugaban hukumar Sibil Defens, DC Apollos Dandaura, a garin Lafiya, birnin jihar Nasarawa.

An tattaro cewa yan bindigan dauke da bindigogin AK-47 sun dira gidan matar ne suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin sukayi awon gaba da ita.

Kakakin hukumar na jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace sun bazama nemansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262