Mijina Ba Ya Kula Da Ni, Na Gaji, Wata Mata Ta Nemi Kotun Shari'a Ta Raba Aurensu
- Wata matar aure uwa ga yara hudu, Kafayat Yusuf, ta nemi Kotun shari'a a Kaduna ta raba aureta sakamakon mijin ya gudu ya barsu
- Matar ta faɗa wa kotun cewa uban 'yayanta, Abdulwahab Yusuf, ga sakar mata ragamar nauye-nauyen aure baki ɗaya
- Duk da mutumin bai halarci zaman Kotun ba, lauyansa ya nemi Alkali ya ƙara masa lokaci domin ya tuntubi wanda yake kare wa
Kaduna - Wata matar aure mahaifiyar mutum huɗu, Kafayat Yusuf, a ranar Laraba ta maka mijinta, Abdulwahab Yusuf, a gaban Kotun shari'ar Musulunci dake zama a Magajin Gari, Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Matar ta nemi Kotun ta raba auren saboda Maigidanta ba ya kula da ita ko kaɗan kuma babu wani tallafi daga 'yan uwansa.
Kafayat ta shaida wa Kotu cewa Yusuf ya watsar da ita da 'ya'yan da Allah ya azurtasu da samu tsawon watanni 9 ba tare da ya waiwayi halin da suke ciki ba.
A kalamanta, matar tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya bar baki ɗaya nauye-nauyen aure kama daga ciyarwa, biyan kuɗin haya, da kuɗin makarantar yara a kaina. 'Yan uwansa ba su nuna wata alamar damuwa ko su tallafa mana ba."
"Na gaji da wannan auren, ina rokon Kotu ta taimaka ta raba mu kawai."
Shin wanda ake zargi ya amsa laifukansa?
A ɓangaren magindanci wanda bai halarci zaman Kotun ba, lauyansa Malam Abdulbasit Sulaiman, ya bayyana cewa ya nemi wanda yake karewa ta wayar salula amma bai same shi ba.
Sai dai Lauyan ya roki Kotu da ta ba shi wani lokaci domin ya tuntubi wanda ake tuhuma don su tattauna kan lamarin.
Bayan sauraron haka, Alkalin Kotun mai sharia Malam Rilwanu Kyaudai, ya sanar da ɗaga sauraron ƙarar har zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba, 2022.
A.wani labarin kuma Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu
Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ranar Litinin ya roki Kotun Kostumare dake zama a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, ta raba aurensa da Matarsa mai suna Joyce a takaice.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Magidancin ya roki Kotu ta datse igiyoyin aurensu ne bisa zargin ya kamata dumu-dumu tana saduwa da ɗan uwansa.
Asali: Legit.ng