Marigayi Sheikh Abubakar Gumi, Ado Bayero da Wasu Sun Samu Lambar Yabon 'Danfodiyo'

Marigayi Sheikh Abubakar Gumi, Ado Bayero da Wasu Sun Samu Lambar Yabon 'Danfodiyo'

  • A makon Ɗanfodiyo da aka gudanar a Sakkwato, an karrama manyan Malamai da wasu mutane bisa ayyukansu nagari ga Musulunci
  • Marigayi Sheikh Abubakar da Ado Bayero na daga cikin waɗanda Masarautar Sarkin Musulmi ta karrama da lambar Yabon Ɗanfodiyo
  • Da yake jawabi a wurin, dan Sheikh Abubakar Gumi, Dakta Ahmad, ya roki Sarkin Musulmi ya tara shugabannin ƙungiyoyin musulunci

Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sarkin Kano na 13, Marigayi Ado Bayero na cikin mutanen da suka karɓi babbar Lambar yabon Sheikh Usmanu Danfodiyo, kamar yadda rahoton Dailytrust ya tabbatar.

Yayin da Gumi wanda ya rike Grand Khadi na jihar arewa da aka rushe, ya samu lambar karammawar Ɗanfodio bisa jagoranci abin koyi, Marigayi Sarkin Kano ya karbi karramawar Sultan Muhammad Bello, bisa shugabanci nagari.

Danfodiyo.
Marigayi Sheikh Abubakar Gumi, Ado Bayero da Wasu Sun Samu Lambar Yabon 'Danfodiyo' Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sauran waɗanda suka samu lambar yabon sun haɗa da Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh, wanda aka karrama da lambar yabon Sheikh Abdullahi Fodiyo kan ilimi da Tallafin karatu.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Alhaja Lateefat, ga karɓi lambar Nana Asma'u bisa aikin inganta walwala yayin da Madawakin Gwandu, Idris Koko, ya samu karramawar Sultan Abubakar III kan ayyukan al'umma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika an karrama Imam Fo’ad Adeyemi da babbar lambar yabon Sultan Muhammadu Sa’ad sakamakon kokarin gina zaman lafiya mai ɗorewa.

Da yake jawabi a wurin bikin da aka shirya a babban ɗakin taron ƙasa da ƙasa a Sakkwato, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, yace waɗanda aka zakulo aka karrama sun yi wa al'umma ayyuka nagari.

A kalamansa, Sarkin Musulmin ya tuna yadda Fitaccen Malamin Musuluncin Mazaunin Kaduna da Marigayi Sarki suka ba da rayuwarsu wajen cigaban Musulunci, al'ummarsu da Najeriya baki ɗaya.

Sultan Sa'ad ya roki kananan yara masu tasowa su maida hankali wurin neman ilimi domin itace kaɗai hanyar yaƙar maƙiya.

Ya yi kira ga haɗin kan ɗaukacin al'umma da Najeriya baki ɗaya, inda ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka karrama ba 'yan yankin Masarutar Sarkin Musulmi bane.

Ya kamata a kira taron kungiyoyin Musulmai - Ahmad Gumi

Da yake jawabi a madadin mutanen da aka karrama, Sheikh Ahmad Gumi, Ɗan marigayi Abubakar Gumi, ya roki Sarkin Musulmi ya kira taron ƙungiyoyin addinin Mussulunci da nufin ɗinke banbancin dake tsakaninsu.

"Wannan shi ne abinda mahaifinka, Marigayi Sultan Abubakar na III ya yi a zamanin rayuwarsa," inji shi.

Legit.ng Hausa ta gano cewa an shirya bikin ne a wani ɓangaren makon Ɗanfodiyo, wanda majalisar Sarkin musulmi da wasu ƙungiyoyi suka ɗauki nauyi.

A wani labarin kuma Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 Da Shugaba Buhari Ya Baiwa Lambar Karramawa Ta Kasa

Gwamnatin tarayya ta gudanar da bikin raba lambobin karramawa ga wasu zaba'bbun ‘Yan Najeriya bisa gudunmuwar da suka baiwa kasar.

Da cikin sama da mutum dari hudu da aka karrama,, gwamnati ta haɗa da wasu manyan Malamai guda, mun haɗa muku su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel