Masu Damfara Sun Shiga Uku Yayin Da EFCC Ta Musu Tonon Silili, Ta Aike Da Saƙo Mai Muhimmanci Ga Ƴan Najeriya
- An shawarci yan Najeriya su dena amfani da wayoyin sata ko siya saboda dalilan tsaro, a cewar EFCC
- A cewar hukumar, wadanda aka sace wa wayoyinsu su yi gaggawan zuwa banki su toshe asusun bankunansu
- Hukumar ta EFCC ta bada wannan shawarar ne yayin da ta ke cewa yan damfarar za su iya samun damar shiga asusun bankunansu da wayoyin sata
Sokoto - A ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, Hukumar yaki da rashawa EFCC ta shawarci yan Najeriya wadanda aka sace wa waya su garzaya bankinsu domin a toshe asusunsu.
Shugaban EFCC na yankin Sokoto, Aliyu Yunusa, ne ya bada wannan shawarar yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
EFCC ta gano manyan hanyoyi biyu da ake yin damfara
Yunusa, wanda ya yi magana kan karuwar damfara masu alaka da ATM da aka sace a Sokoto, ya bayyana manyan hanyoyi biyu da ake yin irin wannan damfarar.
Hanya ta farko shine, "Canja ATM" wanda ke faruwa a lokacin da kwastomomi suka tafi ATM cire kudi ko POS inda masu yaudarar za su yi yunkurin cewa za su taimakawa mutane cire kudi a ATM.
Ya ce:
"Wadanda ake zargin galibi zuwa suke yi kamar za su taimaki mutane wurin cire kudi a ATM ta hakan zai su canja musu kati su basu wanda baya aiki.
"Bayan sauya katin da haddace lambar sirri na katin, mai damfarar na iya cewa matsalar sabis ne sai ya mika wa katin da ya riga ya canja ga mai shi kuma ya yi tafiyarsa.
"Dan damfarar sai ya tafi wani ATM din daban ya cire dukkan kudin da ke asusun wanda ya damfara ko ya tura wani asusun."
Hanya ta biyu
Hanya ta biyu da ake damfarar, a cewarsa, shine 'Satar Wayar Salula'.
"A wannan karon, a kan sayar da wayar da aka sace ga yan damfara wadanda za su yi amfani da USSD su gano bayan mutum na banki.
"Hakan zai taimaka musu sanin inda bankin ka ya ke, amma ga dan damfarar da bai kware ba, zai ta gwada lambar USSD na bankuna har sai ya yi nasara.
"Sannan su yi amfani da lambar USSID na banki. Su tura kudin asusun ku zuwa wani asusun daban, galibi zuwa asusun wani da suke riga suka sace katinsa kuma sun san lamban sirrinsa."
Sako ga yan Najeriya
Ya shawarci al'umma su rika kokari suna kare bayanansu na sirri musamman lambar sirri na ATM, BVN da NIN da wayoyin salularsu.
A bangare guda, hukumar ta kama wani Yahaya Umar Shagari wanda ke yi wa jami'an tsaro sojan gona yana damfarar mutane.
An Kama Dan Takarar Jam'iyyar Kwankwaso da Tsabar Kudi N326m da Daloli $610,500
Hukumar EFCC ta kama dan takarar kujerar dan majalisar dokokin jihar Kogi a karkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Ismaila Atumeyi.
Jaridar Punch ta rahoto cewa an kama Atumeyi ne da tsabar kudi har naira miliyan 326 da kuma dala 140,500.
An kama Atumeyi wanda ke son wakiltan mazabar Ankpa 11 a majalisar dokokin jihar Kogi a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, tare da wani Joshua Dominic, wanda ake zargin madugun mai damfara ne.
Asali: Legit.ng